Kotun Majisatare a Kano ta dage shari’ar matar auren nan Hafsat Surajo (Hafsat Chuchu), wadda ake zargin ta yi wa wani matashi mai suna Nafiu Hafizu kisan gilla.
A ranar Litinin ne kotun da ke zamanta a unguwar Yankaba da dage zamanta zuwa ranar 18 ga watan nan na Janairu domin sauraron bukatar belin Hafsat Chuchu kan zargin kisan matashin, wanda abokinta ne.
Mai Shari’a Hadiza Abdulrahman, ta kuma ta ba da umarnin mayar da wadana ake zargin gidan yari ne bayan lauyoyinsu Rabiu Sidi da Rabiu Abdullahi sun nemi a ba da belinsu.
An gurfanar da Hafsat Chuchu ne a tare da mijinta Dayyabu Abdullahi da wasu mutum biyu da suka hada da malamain da ya yi wa gawar Nafiu wanka da kuma mai gadin gidan ma’auaratan.
Kotun ta ba da umarnin a mayar da wadanda ake zargi gidan yari zuwa ranar zama na gaba.
An gurfanar da Hafsat kan zargin aikata kisa da kuma yunkurin kashe kanta, zargin da ta musa a gaban kotu.
Da farko, a hannun ’yan sanda ta amsa cewa ita ce ta kashe Nafiu ta hanyar sossoka masa wuka saboda ya hana ta ta kashe kanta.
Sauran mutum ukun kuma ana zargin su ne da hada baki wajen aikata laifi, boye laifi da kuma ba da shaidar karya.
A ranar 27 ga Disamba, 2023 ne aka fara gurafnar da su, inda Mai Shari’a Hadiza Abdulrahman ta sa a tsare su a gidan yari kafin zama na gaba.