’Yan uwan mutanen da jirgin soja ya kashe a taron Mauludi a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna sun maka Gwamnatin Tarayya a kotu suna neman diyya.
Premium Times ta ruwaito cewa ’yan uwan mutum 53 daga cikin wadanda suka mutu a harin ne suka maka gwamnati a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna suna neman diyyar biliyan 33.
Lauyan masu kara, Mukhtar Usman, ya ce, wadanda ake kara su ne Gwamnatin Tarayya, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya da kuma Antoni-Janar na Kasa.
Suna neman kotun ta ayyana harin a matsayin haramtacce da tauye hakkin wadanda aka kashe, don haka, suke neman “a biya dangin wadana aka kashe ba bisa ka’ida ba diyya.”
- Hayaniya ta kaure a Majalisar Kano kan kudaden masarautu
- Najeriya za ta tura jirage marasa matuka a kan iyakokinta
Suna kuma rokon kotun ta tilasta wallafa sakon ban hakuri a manyan jaridu uku, sannan ta rika biyan kudin ruwan da ke kan kudin, har zuwa lokacin da za ta kammala biyan diyyar.
Kimanin mutum 120 ne dai aka kashe a harin bom din da jirgi mara matuku na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya kai wa mahalarta taron Mauludin a ranar 3 ga watan nan na Disamba.
Tuni dai rundunar sojin ta dauki alhakin harin, wanda ta ce bisa kuskure jirginta ya kai, a lokacin da yake fatattakan ’yan ta’adda.
Harin dai ya ja wa sojojin caccaka tare da fama kaikayin ciwon hare-haren kuskure 15 da jiragen soji suka kai wa fararen hula a kasar daga 2014 zuwa yanzu.
Haka kuma kungiyoyi da daidaikun mutane sun yi ta kira ga gwamnati ta biya diyya, sannan ta gudanar da bincike tare da hukunta duk masu hannu a harin.
Wasu dai na zargin da gangan aka kai harin, wasu na ganin sa a matsayin sakaci ko tsautsayi, ko kuma alamar rashin kwarewa wajen sarrafa jirage marasa matuka a bangaren rundunar.
Gwamnatin Tarayya ta nuna alhininta game da harin, inda a wata hira da BBC, Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce gwamnati za ta biya diyya.
Ministocin Tsaro da manyan jami’an gwamnati ciki har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, sun kai ziyarar jaje kauyen Tudun Biri da kuma asibitin da aka kwantar da wadanda suka jikkata.
Duk da alkawuran gwamnati na yin abin da ya kamata, da kuma umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da bincike da gano masu laifi da hukunta su domin hana aukuwar hakan a nan gaba, kungiyoyin lauyoyin Arewa sun yi alkawarin maka gwamnati a kotu na ganin ta biya diyyar da ya kamata tare da daukar nauyin iyalan duk wadanda harin ya shafa.