Shugabannin Fulani a yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya sun ce ba ruwaito kalamansu daidai ba a rahotannin da aka bayar cewa sun yafe wa wadanda suka kashe wasu matafiya sama da 25 a Jos.
Maganar yafiyar ta shugabannin Fulanin dai ta samo asali ne daga wata sanrwa da Gwamnatin Jihar Filato ta fitar bayan wata tawaga ta yi wa wadanda suka yi rauni rakiya a karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar, Farfesa Danladi Atu.
Wanda aka ambato yana ba da sanarwar yafiyar, Alhaji Muhammad Kabir, Sarkin Fulanin Abeokuta kuma Shugaban Miyetti Allah na Yankin Kudu Maso Yamma, ya bayyana wa Abbas Dalibi hakikanin abin da ya fada, amma ya fara ne da bayani a kan yadda ganarwar ta gudana.
SAURARI: Abin da Ya Faru A Afghanistan Zai Yiwu A Najeriya?