Gamayyar kungiyoyin malamai da dattawa na Jihar Filato sun gargadi al’ummar musulmin jihar a kan kada su sha alwashin ramuwar gayya a kan kowa game da kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya a Jos, babban birnin Jihar.
Hakan na kunshe cikin wata takarda da Sakataren Kungiyar, Ahmad Muhammad Ashir ya rattaba wa hannu.
- Kisan Jibiya: Ku dauki makami ku kare kanku —Masari
- Afghanistan: Amurka ta gana da Gwamnatin Taliban
A cewarsa, musulunci bai taba goyon bayan ramuwar gayya ba a yayin da wasu ke hasashen hakan biyo bayan kisan wasu matafiya da aka yi a Jos ranar Asabar.
A kan haka ne ya gargadi al’ummar Musulmi da su nisanci daukar doka a hannunsu da sunan daukar fansa a kan kisan matafiyan da aka yi.
“Duk da cewa abin da ya faru ya girgizamu ya kuma daga mana hankali matuka, amma hakan ba zai sa mu dauki fansa a kan wadanda basu ji basu gani ba.
“Mu a kungiyance mun yi Allah wadai da wannan mummunan al’amari sannan muna kira ga gwamnati da ta gaggauta kamo wadanda suka yi wannan aika-aika don su dandani fushin kuliya.
“Saboda haka gammayar kungiyoyin na kira ga musulmin Filato da su kwantar da hankalinsu kar su dauki doka a hannunsu.
“Kuma muna jinjina wa jami’an tsaro saboda gaggawar daukar mataki da suka yi bayan faruwar lamarin.
“Kuma muna mika godiya ga Gwamna Simon Lalong da takwaransa na Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da kuma Shugaba Muhammadu Buhari saboda matakin da suka dauka a kan kare kara faruwan abin agaba.
Aminiya ta ruwaito cewa, an kashe matafiyan ne a hanyarsu ta komawa Jihohin Ondo da Ekiti da kuma kasar Ghana bayan sun halarci taron bikin Sabuwar Shekarar Musulunci a Jihar Bauchi.
Bayan isowar matafiyan yankin Gada-Biyu da ke garin Jos, aka tare motocinsu inda aka yi wa wasunsu kisan gilla, wasu kuma suka tsallake rijiya da baya.
Hukumomin ’yan sanda sun zargi ’yan kabilar Irigwe da ke yankin da kai harin, a yayin da kungiyar ’yan kabilar Irigwe ta kasa ta la’anci maharan.
Yankin ya yi fama da rikice-rikice a baya-bayan nan, inda aka yi ta kai hare-haren daukar fansa tsakanin ’yan kabilar ta Irigwe da Fulani.