✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kisan manoma 45: Ran Buhari ya baci matuka —Garba Shehu

Shugaba Buhari ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan manoman.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kisan manoma 45 da aka yi a wani rikici a kananan hukumomin Lafia, Obi da Awe na Jihar Nasarawa a matsayin rashin imani.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu, ya fitar, inda ya ce Buhari ya nuna bacin ransa.

A cewarsa, Buhari ya jajanta wa iyalan wadanda aka kashe tare da wadanda suka ji rauni, sannan ya yi tir da harin.

Shugaba Buhari ya ba wa jama’a tabbacin cewa gwamnatinsa na kokari wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

Ya kuma ce dole sai an bankado bata-garin da suka yi wannan danyen aiki, don su girbi abin da suka shuka.

Har wa yau, ya aike da sakon jaje ga wadanda lamarin ya rutsa da su, sannan ya umarci gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa kan dakile sake faruwar harin, tare da gudanar da binciken da ya kamata.

Buhari ya bayyana cewa daukacin al’ummar Najeriya na tare da iyalan mutnen da aka kashe kuma suna jajanta musu kan wannan danyen aiki da aka musu.