✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Malcom X: Za a biya mutanen da aka daure diyyar $35m

Gwamnatin Amurka za ta biya mutum biyu da aka daure bisa kuskure kan zargin kisan Malcom X diyyar Dala miliyan 35

Gwamnatin Jihar New York ta Amurka za ta biya diyyar Dala miliyan 35 ga wasu mutane biyu da kotu ta daure bisa kuskure kan zargin kashe fitaccen dan gwagwarmaya Malcom X a shekarar 1965.

Kakakin bangaren kula da al’amuran shari’a na Jihar New York, Nick Paollucci, ne ya bayyana haka ga jaridar New York Times a hirar da suka yi a daren Lahadi.

An daure Muhammad Aziz da kuma Khalil Islam ne a shekarar 1965 a bisa zargin kisan wani fitaccen dan Amurka bakar fata, Abdulaziz Al Shabbaz wanda aka fi sani da Malcom X.

A shekarar 2021 wata kotu a jihar ta sake duba shari’ar, sannan ta wanke su, bayan sun shafe sama shekara 20 a gidan yari, da kuma shekara 55 cikin zargi.

Bayan wanke su, Aziz mai shekara 84 a yanzu, ya nemi diyyar Dala miliyan 40.

Shi ma Khalil Islam, wanda ya rasu a 2009 yana mai shekara 74, iyalansa sun nemi diyya a wurin gwamnati.

Malcom X, ya musulunta a shekarun 1960, fitaccen dan gwagwarmaya ne da kuma yaki da wariyar launin fata.

An yi mishi kisan gilla ne tare da matarasa da kuma ’ya’yansa, a lokacin da ya je gabatar da jawabi a wai gangami a Harlem — laifin da aka dora wa mutanen biyu.

Cikon na ukun da ake zargi, mai suna Abdul Halim ya amsa lafin, an kuma daure shi rai-da-rai.

A halin yanzu shekarunsa 81, kuma tun a lokacin da aka fara tsare su ya tsame saurn biyu daga laifin amma ba a sake su ba.