Gwamnatin Jihar New York ta Amurka za ta biya diyyar Dala miliyan 35 ga wasu mutane biyu da kotu ta daure bisa kuskure kan zargin kashe fitaccen dan gwagwarmaya Malcom X a shekarar 1965.
Kakakin bangaren kula da al’amuran shari’a na Jihar New York, Nick Paollucci, ne ya bayyana haka ga jaridar New York Times a hirar da suka yi a daren Lahadi.
- Amurka ta yaba da matakan tsaro a Abuja
- Amurka za ta ba mutanen da ambaliya ta shafa a Najeriya Dala miliyan daya
An daure Muhammad Aziz da kuma Khalil Islam ne a shekarar 1965 a bisa zargin kisan wani fitaccen dan Amurka bakar fata, Abdulaziz Al Shabbaz wanda aka fi sani da Malcom X.
A shekarar 2021 wata kotu a jihar ta sake duba shari’ar, sannan ta wanke su, bayan sun shafe sama shekara 20 a gidan yari, da kuma shekara 55 cikin zargi.
Bayan wanke su, Aziz mai shekara 84 a yanzu, ya nemi diyyar Dala miliyan 40.
Shi ma Khalil Islam, wanda ya rasu a 2009 yana mai shekara 74, iyalansa sun nemi diyya a wurin gwamnati.
Malcom X, ya musulunta a shekarun 1960, fitaccen dan gwagwarmaya ne da kuma yaki da wariyar launin fata.
An yi mishi kisan gilla ne tare da matarasa da kuma ’ya’yansa, a lokacin da ya je gabatar da jawabi a wai gangami a Harlem — laifin da aka dora wa mutanen biyu.
Cikon na ukun da ake zargi, mai suna Abdul Halim ya amsa lafin, an kuma daure shi rai-da-rai.
A halin yanzu shekarunsa 81, kuma tun a lokacin da aka fara tsare su ya tsame saurn biyu daga laifin amma ba a sake su ba.