✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan kiyashi ga Musulmin Rohingya: Suu Kyi ta gurfana a Kotun Duniya

Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta gurfana a gaban Kotun Duniya da ke birnin Hague na kasar Holland, domin kare kasarta daga zargin…

Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta gurfana a gaban Kotun Duniya da ke birnin Hague na kasar Holland, domin kare kasarta daga zargin aikata laifuffukan kisan kiyashi a kan al’ummar Musulmi, ’yan kabilar Rohingya.

Kasar Gambiya ce ta shigar da kara a gaban kotun, tana nuni da cewa ta dauki wannan mataki ne a matsayinta na kasa mai son ganin an tabbatar da adalci da kare al’ummar Rohingya da ta ce hukumomin Myanmar na yi wa kisan kiyashi duk da kasancewarsu ’yan kasar, kuma duniya ta zuba idanu kawai.

A zaman da aka yi na kwana uku, kasar Gambiya da ke Afirka ta Yamma, ta bayyana dalilanta na bukatar alkalan Kotun Duniya su hanzarta shiga wannan lamari da ta ce hukumomin Myanmar  na yi wa al’ummarsu ta kabilar Rohingya, wadanda Musulmi ne kisan kiyashi.

Baya ga haka kasar Gambiya za ta nemi masu shari’a a Kotun Duniyar su dauki matakin ganin hukumomin Myanmar ba su batar ko lalata duk wata shaida ta aikata laifin kisan kiyashi ba a kan al’ummar Rohingya da ke Lardin Rakhine na kasar Myanmar.

Mutumin da ke kan gaba wajen wannan hobbasa a karar, shi ne Ministan Shari’a na Gambiya, Abubacarr Tambadou.

Gidan Rediyon BBC ya tambaye shi dalilin kasarsa na yin wannan ta-maza yayin da ake da sauran kasashe 149 da suka rattaba hannu a kan dokokin duniya na yaki da kisan kiyashi, amma ba wadda ta yi wannan yunkuri sai, ’yar karamar kasarsa, Gambiya, inda ya ce: “Me ya sa Gambiya ba za ta yi ba, me zai sa mu zura ido, kawai mu nemi wasu su yi wannan aiki, alhalin mu ma za mu iya, me zai hana?

“Dokokin duniya ba wai kawai na kasashe masu arziki da karfin soja ba ne kawai, na dukkan kasashe ne masu ’yancin kai.

“Ba ka bukatar sai kana da karfin soja ko na tattalin arziki, kafin ka nemi a yi adalci, ka yi abin da ya kamata. To a nan Gambiya tana amfani da muryarta ce da ta dace ta yi Allah-wadai da wannan kisan kiyashi da Myanmar take yi ga jama’arta.

“Kuma ina ganin wajibi ne kasashen duniya su yi haka. Duniya ta juya wa Rwanda baya a 1994 yanzu kuma muna sake juya wa Rohingya baya,’’ inji Ministan.

Wani kwamiti na musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta tura domin ya gudanar da bincike kan lamarin ya bayyana cewa dubban jama’a ne daga ’yan kabilar ta Rohingya, Musulmi,  bisa dole suka bar gidajensu, suka fake a sansanonin gudun hijira a makwabciyar kasar Bangladesh, saboda matsanantan manufofi na gwamnatin Myanmar.

Tun farko masu gabatar da kara a Majalisar Dinkin Duniya sun zargi sojojin Myanmar da yunkurin karar da kabilar Rohingya a shekarar 2017, mummunan al’amarin da ya sanya fararen hula da dama suka tsere zuwa kasar Bangaladesh don zaman gudun hijira.

Wani bincike da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka gudanar ya bayyana yadda sojojin Myammar suka yi wa mata da kananan yara na kabilar Rohingya fyade da kuma yi wa maza dauri a gidajen yari, zargin da sojojin da gwamnatin kasar suka yi watsi da shi.

Yanzu haka dai ofishin jagora Suu Kyi ya raba wa manema labarai sanarwar aniyarta ta martaba kasar yayin saurararon karar.

A wancan lokaci dai kusan mutum miliyan guda daga ’yan kabilar ta Rohingya ne suka tsere daga kasar inda kimanin dubu 740 ke gudun hijira a Bangladesh.

Guda cikin jagororin ’yan kabilar Rohingya a sansanin ’yan gudun hijira da ke Bangladesh Sayed Ulla ya ce Suu Kyi ba ta da wata hujja da za ta kare kanta.

’Yan gudun hijirar Rohingya na da ra’ayin cewa Suu Kyi na da cikakkiyar masaniya baya ga nuna goyon baya ga cin zarafi da musguna wa da kuma kisan gillar da suka rika fuskanta a Jihar Rakhine.

Saida Khatun daya daga cikin ’yan gudun hijirar wadda a gaban idonta sojin Myanmar suka yi wa mijinta da ’ya’yanta uku da mahaifanta kisan gilla, ta ce suna fatar yi wa Shugabar Gwamnatin Myanmar da manyan sojojin kasar hukunci mai tsanani.

Aung San Suu Kyi da kanta ce take kokarin kare kasar game da wannan tuhuma da kasar Gambiya ta shigar a madadin al’ummar Rohingya kan zargin Myanmar ta karya yarjejeniyar kasa-da-kasa da aka amince da ita a 1948 da take hukunta wanda ya aikata kisan kare dangi.