✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan direban Tasi: Kotu ce za ta raba mu da sojoji —Iyalai

Iyalan sun ce za su tafi kotu don neman diyyar kashe direban da aka yi.

Iyalan wani direban tasi da sojoji suka kashe a Jihar Filato, sun ce har yanzu ba su binne shi ba, sai kotu ta kwato musu hakki a hannun sojoji.

Dan uwan mamacin, Abdullahi Karafa, ya shaida wa Aminiya cewa a halin yanzu suna gudanar da bincike domin zuwa kotu domin karbar diyyar dan uwan nasa, shi ya sa har yanzu ba su binne shi ba.

Abdullahi ya ce mamacin mai suna Abubakar Abdullahi Karafa, mutum ne mai karamin karfi kuma shi ne yake kula da mahaifiyarsa da ’ya’yansa hudu, sannan a lokuta da dama sai ya fita yake samo musu abin da za su sa a bakin salati.

Ya kara da cewa “Baya ga tuhuma kan kashe shi da aka yi, muna neman diyya saboda ’ya’yansa da ya bari.

“Mun dauki lauyoyi wadanda su ne suka ba da shawarar kada a binne shi har sai an kammala bincike”, inji shi.

A ranar Asabar Aminiya ta rawaito yadda sojojin Rundunar ‘Operation Safe Haven’ suka lakada wa wani direban tasi dukan da ya yi ajalinsa a lokacin da yake dawowa daga Karamar Hukumar Mangu a Jihar.

A ranar Lahadi, rundunar ta Operation Safe Heaven ta ce ta samu rahoton kisan da ake zargin dakarunta da aikatawa, kuma ta dauki alkawarin gudanar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Babban Kwamandan da ke jagoranta Babbar Runduna ta 3 ta Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar Ibrahim Ali, ya ziyarci iyalan mamacin domin jajanta musu.