Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya yi kira ga matasan garin Gashuwa da su mayar da wukakensu cikin kube bisa zanga-zangar da su ke yi kan kashe wani direban babbar mota da ake zargin sojoji da yi.
Aminiya ta rawaito yadda matasan garin na Gashuwa suka fusata sannan suka fantsama tituna suna zanga-zanga tare da kone-kone a ranar Asabar, don nuna fushinsu a kan lamarin.
- Majalisar Dinkin Duniya na so a binciki harin da Saudiyya ta kai Yemen
- An tsare shanu 44 a Bayelsa saboda karya dokar hana kiwo ta Jihar
To sai dai a cewar wata sanarwar ta bakin mai magana da yawun Gwamnan, Alhaji Mamman Muhammad, Mai Mala Buni ya ce tuni ya ba da umarnin da gudanar da bincike kan lamari cikin gaggawa don daukar matakinn da ya dace a kai.
“Gwamnan ya kwatanta wannan abu da ya faru na bindige wannan direba da abun takaici, musamman lura da yadda muka fara farfadowa daga halin da muka shiga a baya dangane da matsalar tsaro a dukannin fadin Jihar.
“Don haka, da mu gwamnati da kuma hukumomin tsaro ba za mu taba lamuntar duk abin da zai kawo mana koma baya ba a harkokin tsaro.
“Saboda haka, na ba da umarnin gudanar da cikakken bincike dangane da wannan abin da ya faru don ganin an yi abin da ya dace don kaucewa faruwar irin ya haka a nan gaba.
“Ina kuma kira da babbar murya ga dukkannin al’ummar Karamar Hukumar ta Bade da ma illahirin al’ummar Jihar da su zama masu bin doka da oda.”
“Ya kamata mu yi watsi da duk wani abu da zai haifar mana barazana dangane da yanayin zaman lafiyarmu, kamar yadda Allah SWT ya shar’anta mana na mu guji ta da fitina a matsayin mu na musulmai,” inji Gwamnan.
Daga nan sai ya yi addu’ar Allah Ya jikan direban da ya rasu, Ya kuma ba iyalansa hakurin jure rashinsa.