Kotu a Jihar Kano ta tisa keyar wata matar auren da ake zargi da kisan ma’aikacin gidanta mai suna Nafiu Hafiz Gorondo zuwa gidan yari.
An gurfanar da matar a gaban Babar Kotun Majistare da ke zamanta a Yankaba bisa zargin ta da caccaka wa marigayin wuka lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
Mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnati jihar, Barista Lamido Sorondinki ya shaida wa kotun cewa ana tuhumar matar da laifuka biyu na kokarin kishe kanta da kuma yi wa wani kisan gilla, laifukan da suka saba da sashe na 281 da na 221 na Kundin Pinal Kod.
A cewar Barista Lamido Sorondinki wacce ake zargin ta yi amfani da wuka mai kaifi don kashe kanta inda ta yanke hannunta na hagu.
- ’Yan bindiga sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa a Taraba
- HOTUNA: Jana’izar tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Ghali Na’Abba
“A lokacin ne ta yi amfani da wannan wukar ta caka wa Nafiu Hafizu a kahon zuciya, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa,” in ji shi.
Wacce ake zargin ta amsa aikata laifi na farko yayin da ta musanta aikata laifi na biyu.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Hadiza Abdurrahman ta bayar da umarnin tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu, 2024.
Kotun ta kuma gurfanar da karin mutane uku, ciki har da mijin wadda ake zargin bisa zargin sun taimaka mata wajen aikata laifi da kuma boye gaskiya da bayar da bayanan karya game da dalilin rasuwar marigayi Nafiu.
“Wadanda ake zargin sun yi amfani da bayanan karya wajen sanar da ’yan uwan Nafiu game da dalilin rasuwarsa inda suka ce ya rasu ne dalilin aikin basir da aka yi masa,” in ji mai gabatar da kara.
Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zargin su, da suka saba da sashe na 97 da 277 da 178 na Kundin Pinal Kod.
Su ma alklalin kotun Hadiza Abdurrahman ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Janairu, 2024.