✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan cocin Ozubulo: Osinbajo ya tura tawagar ministoci biyar Jihar Anambara

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya tura tawagar jami’an gwamnati biyar zuwa Jihar Anambara don su jajantawa gwamnati da kuma al’ummar jihar kan kisan gillar…

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya tura tawagar jami’an gwamnati biyar zuwa Jihar Anambara don su jajantawa gwamnati da kuma al’ummar jihar kan kisan gillar da aka yi wa membobin Cocin Darikar Katolika ta Saint Philips a ranar Lahadin da ta gabata a garin Ozubulu da ke karamar hukumar Ekwusigo.
Mai Magana da Yawun Osinbajo, Laolu Akande a wata sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa tawagar ta kunshi Ministan Kwadago, Chris Ngige da na Lafiya Isaac Adewole da kuma na Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama da kuma Minista a ma’aikatan Muhalli, Jubrin Ibrahim da kuma Minista a ma’aikatan Ilimi, Anthony Anwuka.
Akande ya ce tawagar za ta mika takardar jaje ta Mukaddashin Shugaban Kasa a madadin gwamnati da al’ummar Najeriya ga Gwamna Willie Obiano.