Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa mutum 710 waɗanda ba ’yan asalin jihar ba, tallafin sufuri domin su koma garuruwansu don yin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara tare da ’yan uwansu.
An ƙaddamar da wannan shiri ne a tashar Borno Express a ranar Asabar, inda aka fara jigilar mutum 285 zuwa wurare daban-daban a faɗin Najeriya.
- Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato
- Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra
Za a ci gaba da wannan jigilar, inda za a sake tashin mutum 285 a ranar Lahadi, yayin da sauran za su bar Maiduguri a ranar Litinin.
Da yake magana yayin ƙaddamar da shirin, shugaban ƙungiyar Ohaneze All Progressives Congress (APC), Cif Ugochukwu Egwidike, ya bayyana cewa kowane daga cikin matafiya 710 zai karɓi tallafin sufuri kyauta tare da kuɗi Naira 50,000.
Haka kuma, mata kimanin 250 da mazansu suka rasu kuma ba za su iya tafiya ba, an tanadar musu da Naira 50,000 kowacce domin gudanar da bikin Kirsimeti.
Cif Egwidike, ya yaba jajircewar Zulum wajen tallafa wa mabuƙata, ya ce shirin zai rage raɗaɗin talauci tare da walwalar al’umma.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Zulum tana ɗaukar nauyin Kiristoci zuwa Kudu domin gudanar da ibada, baya ga tallafin sufuri kyauta da ake bai wa waɗanda ba ’yan asalin jihar ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
“Bugu da ƙari, gwamna Zulum ya taimaka wa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa, ciki har da waɗanda ba ’yan asalin jihar ba.
’Wannan yana nuna irin adalcin gwamna wajen tallafa wa dukkanin jama’a ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.”
Shi ma Sarkin Yarbawa a Jihar Borno, Alhaji Hassan Alao Yusuf, ya yaba wa gwamnan bisa wannan karamcin.
Ya ce tsarin safarar mutane da ba ‘yan asalin jihar ba alama ce ta yadda gwamna ke gudanar da ayyukan alheri ga al’umma.
Mamban kwamitin amintattu na Ohanaeze Ndigbo, Pharm Napoleon Egbonu, ya bayyana cewa irin wannan taimako daga gwamna abin koyi ne ga sauran shugabanni.
Ya ce, “Karamcin Gwamna Zulum zai taimaka wajen tabbatar da haɗin kai da amana tsakanin al’umma a faɗin ƙasar nan.”
Hakazalika, Babban Manajan Kamfanin Sufuri na Borno Express, Grema Zanna, ya yaba wa gwamnan bisa wannan taimako.
Ya bayyana cewa shirin sufuri kyauta na daga cikin dabarun gwamna na rage matsalolin sufuri da tsadar kayan masarufi ga mazauna jihar.