Shugaban Kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya yi wa fursunoni sama da 1,000 afuwa tare da sakin su daga gidajen yari albarkacin bikin Kirsimeti.
Daga cikin 1,004 da aka saki a ranar Litinin akwai ’yan kasar Sri Lanka da aka daure saboda rashin biyan tara, in ji kwamishinan gidan yari Gamini Dissanayake.
Afuwar ta baya-bayan nan na zuwa ne bayan da ’yan sanda suka kama mutum kusan 15,000 a wani samame kan masu ta’amalli da miyagun kwayoyi na tsawon mako guda da ya kare a jajibirin Kirsimeti.
Sanarwar da rundunar ’yan sandan kasar ta fitar ta ce an kama mutum 13,666 da ake zargi yayin da aka tsare kusan 1,100 masu shaye-shaye kuma an tura su gidan gyaran hali.
Sri Lanka ita ce mafi yawan mabiya addinin Buddah kuma shugaban kasar a baya ya yi afuwa ga wadanda aka yanke wa hukunci a watan Mayu don bikin Vesak a kasar.