✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe mahara 14, sun ceto mutum 14

Dakarun sun ceto wasu mutum 14 da maharan suka sace.

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ’yan bindiga 14 a wani samame da suka kai a Jihohin Kaduna da Neja.

Sojojin sun kuma ceto mutum 14 da ’yan bindigar suka sace a yayin gudanar da aikin.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin, Laftanar-Kanar Musa Yahaya, ya ce a ranar Asabar sojojin suka kashe ’yan ta’adda biyu suka kwato bindigu guda biyu kirar AK-47 da babura a yankin Madawaki da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Sojojin sun kuma gano maboyar hatsabibin dan ta’adda Ali Kachalla, amma ya tsere tare da yaransa.

Sojojin sunceto wasu maza 13 da aka sace a ranar 13 ga Oktoba, 2023.

A Kaduna kuma, dakarun sun kashe ’yan ta’adda uku a yankin Madidaro da ke Karamar Hukumar Birnin-Gwari sannan suka kwato bindiga AK-47 da wasu muggan makamai.

A Kidandan-Yadi da ke yankin Birnin-Gwari, kuma sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da lalata sansaninsu sannan suka kwato babura 12.

Kazalika, dakarun sun ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a yankin Maro bayan fafatawa da maharan.

Yayin wani aiki da sojojin suka yi da safiyar Lahadi, sun yi wa ‘yan ta’addan Kwanar Batero da ke Kaduna kwanton bauna tare da kashe daya daga cikinsu, sannan suka kwato makamai da alburusai yayin artabun.

A baya-bayan nan dai dakarun sojin Najeriya na ci gaba da kai wa ‘yan bindiga hari, inda suke ci gaba da kashe su tare da raunata da dama daga cikinsu.