A kokarinta na kare rayuka da dukiyoyi Gombe, Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta girke jami’ai 780 domin sintiri a Jihar Gombe a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar Shekara.
Kwamandan hukumar a jihar, Muhammad Bello Mu’azu, ne ya sanar da hakan, yana mai umurtar Kwamandojin Yankin da na Kananan hukumomi da sauransu cewa su tabbatar sun tura isassun jami’ai a lungu da sakon jihar.
A cewar sanarwar, za a tura jami’an ne a wuraren ibada da kasuwanni da tashohin mota da kuma wuraren shakatawa.
Sannan sai ya bukaci jama’a da su yi bukukuwan a tsanake wajen kiyaye doka da oda domin jami’ansa za su yi aikinsu ba sani, ba sabo.
- Matsahi ya kashe abokinsa saboda na’urar jin sauti a Kano
- Ana zargin mata da miji da yi wa matashi kisan gilla a Kano
A cewarsa, za su tabbatar da ganin sun tsare rayuka da dukiyoyi yadda ya dace kafin lokacin kirsimeti da kuma Sabuwar Shekara.