’Yan kasuwa a Gombe sun koka kan yadda hauhauwar farashin kaji ya jawo karancin ciniki lokacin bikin Kirsimeti.
’Yan kasuwar sun ce tashin farashin kajin ya haura na lokacin Kirsimetin 2021, wanda ya sanya suke tafka asara a bana.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa kasuwannin Gombe sun kasance a cike da masu zuwa cefanen Kirsimeti, sai dai bangaren masu sayar da kaji babu masu ciniki sosai.
Wani dan kasuwa mai suna Kabiru Musa ya bayyana wa Aminiya cewa bara a irin wannan lokacin, kaji 90 ya sayar, amma bana ko 10 har yanzu bai sayar ba.
“Amma wannan ba ya rasa nasaba da yadda kusan kowa ya koma kiwon kaji a gida; Don haka sai dai ka ga mutum ya zo da kajinsa kasuwa a yanka masa.
“A bara mun sayar da kazar da ake cewa Buroila N4,000 da N5,000, amma bana N6,000 zuwa N7,000 muke sayar da ita.
“Kazar gida babba N3,000 da N4,000 take bara, bana kuma sun fara ne daga N4,000 zuwa N6,000.”
Shi ma wani mai yankan kajin mai suna Muhammad Baffa ya ce tabbas ya fi masu sayar da kaji ciniki a bana.
“Duk da cinikin nawa bai kai na 2021, sai dai hakan ba zai hana mu gode wa Allah ba,” in ji shi.
Bulus Joseph da ke sayar da kaji a gidan gonarsa ya ce kaji 50 yayi kiwo, amma ko 18 har yanzu bai sayar ba.
Baya ga Gombe, rahotanni na nuna a sauran kasuwannin Najeriya ma tashin farashin kayan masarufin da na dabbobi, ya sanya bana babu ciniki kamar bara.