Kalubale da tsaiko game da sha’anin tsaro a yankin Kudu Maso Gabas ya dabaibaye harkar sufuri da tafiye-tafiyen da da aka saba duk karshen shekara a lokutan bukukuwan Kirsimeti.
Miliyoyin mutane daga Kudu Maso Gabas da suka saba gudanar da bukukuwa da suka hadar da na al’ada, addini da sauransu tun daga 15 ga watan Disamba har zuwa 15 ga watan Janairun kowace shekara, a bana sun kaurace wa zuwa yakin nasu sakamakon hare-haren ‘yan awaren Biyafara.
- ’Yan Boko Haram sun kone gidaje da rumbunan abinci a Borno
- DAGA LARABA: Yadda Ake Aure Da Ciki A Najeriya
Kazalika, binciken wakilanmu ya gano yadda aka samu mummunan koma-baya ga harkar sufuri a wannan lokaci, wanda hakan ya sa tashoshin motoci da filayen jiragen sama kasancewa babu hada-hada kamar a baya.
Duka wannan na zuwa ne sakamakon hare-haren da ’yan kungiyar awaren Biyafara ke kai wa babu kakkautawa a yankin na Kudu Maso Gabas; wanda ya hadar da kashe mutane, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’adanci.
Kazalika, tsadar farashin kayan masarufi da talauci na daga cikin wasu dalilai da ya sa mutane suka kaurace wa tafiye-tafiye zuwa yankin musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara.
Wani dan kasuwa, Francis Nzediegwu wanda ya angwance a baya-bayan nan, ya ce bai shirya zuwa yankin a watan Disambar nan ba, saboda kudin zirga-zirgar sufuri ya yi tsada.
“Karo na farko cikin shekaru masu yawa ba zan je gida yin bikin Kirsimeti ba,” inji shi.
Shi ma wani Ebuka Ndive da ya zanta da wakilinmu, ya ce wannan ne karo na farko da bai ziyarci yankin ba saboda yanayin da ake ciki.
Shi kuwa wani dan kasuwa mai suna Johnson Ezeliora, wanda ya ziyarci yankin a baya-bayan nan, ya ce yankin ba ya cikin yanayin da ake yayatawa.
“Abubuwa sun ja baya game da harkar kasuwanci, idan na yi tafiya na kan kashe kudade da yawa kuma ban san me sabuwar shekara za ta zo mana da shi ba. Don haka a Legas zan yi bikin Kirsimetin bana.”
Shi kuwa wani dan kasuwa a yankin Okigwe a Jihar Imo, da ya bukaci a sakaya sunansa, cewa ya yi yanayin da jihar ke ciki babu dadi, don babu wanda zai bai wa ‘yan uwansa shawara kawo ziyara.
“Mahara sun dagula kafatanin yankin. Za a iya ganinsu ta ko ina dauke da muggan makamai su farmaki sojoji da jami’an tsaro,” inji shi.
Karancin fasinjoji a tashoshin mota
Bincike a fitacciyar tashar mota ta Jibowu da ke Legas da Babban Birnin Tarayya, ya gano yadda ake ci gaba da samun karancin mutanen da ke yin tafiye-tafiye.
Sai dai wani direban bas, Jude Nwankwo, ya ce suna dai ci gaba da sa ran samun karin fasinjoji daga nan zuwa ranar 24 ga watan na Disamba.
“Ba na tunanin matsalar rashin tsaro ce ta haddasa karancin fasinjojin. Kudin sufuri ya yi tsada sosai. Daga Legas zuwa Nnewi ya kan fara daga 25,000 zuwa 28,000. A Fatakwal ma haka abun yake. A takaice babu inda mutum zai je a Kudu Maso Gabas a kasa da 23,000,” a cewarsa.
Wani fasinja a tashar motar da ya bayyana kansa a matsayin Simeon, ya ce wasu mutane na fakewa da rashin tsaron a yankin suna cutar da ’yan uwansu.
“Matsalar tsaro a yankin ba IPOB ce ta haddasa shi ba. Abin da muka sani shi ne wasu mahara na fakewa da IPOB. Zan yi tafiyata kamar yadda na saba saboda bana tsoron komai,” in ji shi.
Mutanen Kudu mazauna Arewa na dari-darin tafiya
Har wa yau, binciken wakilanmu ya gano yadda ’yan kabilar Igbo mazauna jihohin Arewa irin su Kaduna da Neja da Kano da sauransu ke dari-darin kai ziyara yankin na Kudu Maso Gabas.
Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda matsalar rashin tsaro ke barazana da kwanciyar hankalinsu.
A wani bangaren kuwa, wasu na alakanta tsadar rayuwa da kayan masarufi daga shingen da zai hana su kai ziyara tare da yin bukukuwan karshen shekara kamar yadda suka saba.