Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken: “Kirkin Tsuntsu.” Labarin ya yi nuni ne da yadda kirki ke da muhimmanci a rayuwar dan Adam. A sha karatu lafiya.
Akwai wasu tsuntsaye a kan wata babbar itaciya a wani daji. Ba su da wani gida in ban da shekar da suka yi a kan bishiyar.
Wadannan tsuntsayen sun kasance mata da miji.
Ran nan yunwa ta dame su kuma suka rasa yadda za su yi sai suka yanke shawarar kowa ya fita yawon neman abinci shi kadai ko za su yi sa’a.
Yamma na yi sai ita macen ta dawo sannan ta yi mamakin rashin ganin mijinta. Ta shiga sake-sake a zuciyarta can sai ta ga wani mutum dauke da mijinta a keji.
Ta yi bakin cikin haka kuma ta rasa yadda za ta yi, ga shi ana tafka ruwan sama ga mutumin ya jike sharkaf.
Sai ta yi sauri ta samo kara ta hura masa wuta ta ce ya ji dumi domin ya jike sannan idan ya gama za ta fada cikin wutar ta soyu domin ya samu yin kalaci.
Wannan kirkin da ta yi wa wannan mutum ya sa tausayinta ya kama shi kuma ya sakar mata mijinta daga keji.