Wasu matasan Kiristoci a Karamar Hukumar Kachia da ke Kudancin Kaduna sun hadu tare da Musulmai yayin aikin gyaran Masallacin Idi don shirin gudanar da Sallah Babba.
Matasan, tare da wasu dattawan Kiristocin sun yi aikin gyaran masallacin ne tare da Musulmai don yaukaka zumunci da dangantaka tare da habaka zaman lafiya a yankin, kamar yadda Shugaban matasan Kiristocin, Daniel Bitrus ya shaida wa wakilinmu.
- Limaman cocin da aka gano ‘yaran sata’ fiye da 50 a Ondo sun shiga hannu
- Obasanjo ya yi direban Keke Napep na yini daya
Bitrus, yace wannan shi ne karo na farko a Karamar Hukumar ta Kachia da ma Jihar Kaduna baki daya inda Kiristocin suka zo dauke da fatanya da tsintsiya don aikin masallacin idin na tsawon kwana biyu.
Ya kuma ce za su yi amfani da wannan damar wajen kulla ’yan uwantaka tsakanin mabiya addinan na Musulunci da na Kiristanci.
“Wannan shi ne karo na farko kuma muna fatan ci gaba da hakan kowace shekara. Taimaka wa juna ya zama wajibi musamman a irin halin da muka tsinci kasarmu da yankinmu a ciki,” inji shi.
Jessica Akila, daya daga cikin matan Kiristocin da suka zo aikin gyaran masallacin a ranar Asabar tare da gudummawar kayan aiki da ruwan sha, ta bayyana farin cikinta da wannan ci gaban da suka samar, inda ta karfafa batun hadin kai tsakanin mabiya addinan biyu.
Yayin da yake bayyana farin cikinsa, Sakataren Kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) na Karamar Hukumar, Mallam Ibrahim Tasi’u ya ce Kiristoci da dama ne suka halarci gyaran masallacin na idi inda suka riga Musulman zuwa tare da kayan aikinsu.
Ya ce irin haka bai taba faruwa a tarihin garin Kachia ba, inda ya yi kira ga Musulmai da Kiristoci su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu.
Kudancin Kaduna na daya daga cikin yankunan da suka yi fama da tashe-tashen hankula tun daga shekarun baya har zuwa ’yan kwanakin baya.
Masana dai na ganin irin wannan mataki zai taimaka wajen samar da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci.