Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci.
Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida — namiji ko mace.
A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna:
- Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi.
- Fitar da zakkar fid da kai, wato Zakkar Kono.
- Cin dabino ko abinci kafin zuwa Sallar Idi.
- Yin wankan idi kafin zuwa halartar sallar idi.
- Sanya sabbi ko mafiya kyawtun tufafi da mutum ya mallaka.
- Sanya turare da yanke farce
- Ana son sanya turare ga maza.
- Yawaitawa da kuma bayyana kabarbari ga maza da mata.
- Daina yin kabbarori daga lokacin da aka tayar da sallar.
Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, LaiLaha illAllah, Allahu Akbar walillahil hamdu. - Sauraron huduba bayan kammala Sallar.
- Zuwa sallar da dawowa ta hanyoyi daban-daban.
- Rashin zuwa da makami ko wani abu da zai razana mutane sallar idi.
- Ziyara da taya ’yan uwa da sauran murna.