✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiristoci sun taya Musulmai share Filin Idi a Kudancin Kaduna

Kiristoci sun taya Musulmai share filin Idi a Kudancin Kaduna

A wani bangare na inganta dangantaka tsakanin addinai, wasu Kiristoci sun taya Musulmai share filin Idi a garin Kachiya da ke Jihar Kaduna, a karshen mako.

Mutanen, wadanda suka hada da matasa da dattijai maza da mata dai sun yi fitar dango ne domin nome ciyayin da suka yi girma sosai a filin sakamakon daminar da ake ciki.

Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), reshen Karamar Hukumar Kachiya, Mallam Ibrahim Tasiu, ya bayyana jin dadinsa da yadda Musulamai da Kiristocin suka fita aikin sosai.

Ya kuma yaba wa kokarin Kwamitin Tabbatar da Zaman Lafiya a Tsakanin Addinai (IMC) da Hukumar Tabbatar da Zaman Lafiya ta Jihar Kaduna (KAPECOM) da tawagar Mercy Corps kan irin rawar da suke takawa wajen bunkasa zaman lafiya.

Shi ma Ko’odinetan kungiyar ta IMC a Jihar Kaduna, Samso Auta, ya taya Musulmai murnar Sallah Babba, inda ya yi musu fatan yin shagulgula lafiya.