Tsadar rayuwa da tashin abincin kaji na neman jefa masu kiwon Kaji cikinwani hali inda ake hasashen kiret ɗin ƙwai zai iya Kai wa Naira dubu 10.
Kiret ɗin da a yanzu ake sayar da shi a kan farashin Naira 5,500 zuwa Naira 6,000 na iya kaiwa Naira 10,000, in ji Ƙungiyar Manoman Kaji ta Nijeriya (PAN).
A halin yanzu, Nijeriya na fuskantar matsanancin hauhawar farashin kayayyaki da ba a taɓa ganin irinsa ba tsawon shekaru, inda farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi.
Daga cikin dalilan da suka haddasa wannan hauhawar farashi akwai ƙarin farashin mai da kuma ƙarancin dalar Amurka a kasuwannin canji.
Da yake jawabi a taron manema labarai na bikin Ranar Ƙwai ta Duniya a Abuja, Sakataren Ƙungiyar PAN na Babban Birnin Tarayya (FCT), Musa Hakeem, ya yi kira ga gwamnati da ta ayyana dokar ta-ɓaci a sashen samar da ƙwai.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaugawa ba, wannan tashin farashi zai zama tilas, wanda zai ƙara ta’azzara matsalar ƙarancin cin abinci mai gina jiki a tsakanin ‘yan Najeriya.
Hakeem ya danganta wannan matsalar da tsadar kuɗin sufuri da ta biyo bayan cire tallafin mai, da kuma tsadar abincin kaji sakamakon hauhawar farashin kayan abinci daga hannun masu niƙa kayan abinci.
“Tashin farashin samar da ƙwai na iya sa kiret din ƙwai ya kai Naira 10,000, amma mun bar farashin a kan Naira 5,500 ne saboda tausayi ga masu siya,” in ji shi.
Ya bayyana takaicinsa game da rashin goyon bayan gwamnati, inda ya ce shekarun da suka gabata ne aka taɓa ba da tallafin hatsi ga manoman kaji.
Hakeem ya yi kira ga haɗin kai tsakanin gwamnati da manoman kaji, yana mai cewa ƙungiyar na da cikakkun bayanan manoman kaji da za a iya amfani da su don samar da tallafi kai tsaye.
Shi ma wani dillalin kayan gona, Jude Arikogu, ya bayyana damuwa kan inganci da nauyin abincin kaji, yana mai cewa wasu buhunan 25kg ba su kai nauyin da aka rubuta ba, wanda hakan ke ƙara jefa manoma cikin wahalar gudanar da ayyukansu