✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kira ga Gwamna Ambod

Salam. Aminiya ina so ku taimake ni ku miqa min roqona ga Gwamna Akinwumi Ambode da ya hana barace-barace a Jihar Legas. Domin  yadda darajar…

Salam. Aminiya ina so ku taimake ni ku miqa min roqona ga Gwamna Akinwumi Ambode da ya hana barace-barace a Jihar Legas. Domin  yadda darajar Bahaushe take zubewa saboda ’yan uwammu Hausawa da suke zubar mana da mutumci wajen barace-barace. Za ka ga mata da yara qanana suna yawo, ko kuma da jirirai suna nuna bakinsu wai a ba su na abinci. Kuma wallahi har ma cikin shege ake yi musu yanzu. Don Allah  Bahaushe da ke da daraja da kuma addinin Musuunci, ai addini bai ce mata da yara qanana a riqa xibarsu ana koya musu yawo zuwa jihohin Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu ba. Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji  08111389999, 08096368393

Mu koma ga Allah
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un tabbas ko shakka babu mu al’ummar Arewacin Najeriya muna cikin wani halin da sai dai mu qara dagewa da roqon Allah, tare da gyara tsakanin mu da Allah, ta hanyar istigifari da hailala da salatin Annabi, ko zai kawo mana qarshen zubar da jinin bayin Allah. Ganin yadda wasu xauke da boma-bomai suka far wa al’ummar jihohin Adamawa da Kano, inda suka kashe jama’a da dama.  Don haka muke kira ga gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro su xauki matakin ba sani, ba sabo ga duk wanda aka kama da hannu wajen zubar da jinin bayin Allah  da kai hare-haren ta’addanci. A qarshe muke roqon Allah Ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya a qasar mu baki xayanta, da ma qasashe makwabtan mu. Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999/ 08138203747 [email protected]   

A kashe wuta lokacin hunturu
Assalam. Edita, lallai yanzu mun shiga lokacin sanyi, mu kula da yara masu hura wuta, don jin xumi da zarar sun gama su kasheta. Haka mutanen qauyuka su ma su sa ido akan duk mai hura wuta don kiyaye gidajensu,wanda mafi yawa qirare ne da manoma suka yi qoqarin kwashe amfanin gonakansu, don gudun fataken dare, da aukawar makiyaya gonakinsu. Daga Hussaini Almusaya Gombe, 08130446601

Gargaxi ga ’yan majalisa
Aminiya  ’yar amana  don  Allah   ki miqa min  saqona  ga  ’yan majalisun  qasa  da su sani  rigar  Shugaba Buhari  suka shiga,  suka ci  zave,  amma suna nema  su kauce  daga tsarin  da yake so  ya sa qasar nan a gaba.   To,   su sani shekarar 2019  na zuwa,  mu talakawa muna jiransu.  Daga Musa Unguwar Maiyasin  da Rabi’atu  Xanja Jihar  Katsina 08060611124 08069274090

Ta’aziyya ga Kano da Yola
Assalamu alaikum, Edita ka isar da saqona ga al’ummar Kano da na Yola Jihar Adamawa, bisa rayukan da aka rasa a jihohin dalilin harin bom da aka kai musu,  wanda qungiyar ta’adancin suka kai musu. Allah ya jiqan waxanda suka rasu, Ya bai wa waxanda suka jikkata lafiya.  Daga Bilya Tukur Bakori  09033272527 [email protected]
Ta’aziyyar Prince Audu
Haqiqa mutuwa rigar kowa. Qungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina na yin ta’aziya ga iyalai da ’yan uwa da abokan arzika da masoya da Jam’iyar APC da kuma Gwamnatin Jihar Kogi bisa ga rasuwar Prince Abubakar Abdu. Da fatan Allah Ubangiji Ya jiqansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Allah Ya sa mu cika da imani. Daga Haruna Muhammad Katsina. [email protected] 07039205659

Jinjina ga jam’iyyar APC
Salam Aminiya  Hausa. Jinjina  ga  jam’iyyar  APC  ta qasa    kan  yin nazari  da zaven da aka  gudanar  a  jihar  Kogi  wanda Allah  ya yi  wa  xan takarar Jam’iyyar  APC  marigayi  Alhaji  Abubakar  Audu rasuwa  da  fatan za su  yi  nazari  bisa  adalci da Gaskiya.  08108003333. [email protected]

Ta’aziyyar Aja Gwarzo
Haqiqa mutuwa rigar kowa. Muna yin ta’aziya ga iyalai da ’yan’uwa da abokan arzika da Hukumar gidan rediyo Najeriya ta Kaduna (FRCN), bisa ga rasuwar Alhaji Ahmad Aja Gwarzo Mai gabatar da shirin Wasa Qwaqwalwa da kuma sanarwa.Da fatan Allah Ubangiji Ya jiqansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Ya sa mu cika da imani. Daga Qungiyar Muryar Jama’a.Reshen Jihar Katsina. 07039205659

Ta’aziyyar Prince Audu
Rai Baqon Duniya.  A yau cikin alhini ina miqa saqon ta’aziyyata zuwa ga ‘yan uwa da iyalan marigayi xan takarar gwamnan jihar Kogi wato Alhaji Abubakar Audu.  A gaskiya an yi babban rashi sabili da mutuwa ta yi wa Audu zuwan ba- zata. A vangare guda kuma ina mai jan hankalin ‘yan siyasar Najeriya da su koyi darasi da mutuwar Prince Audu sabili da mutuwa ba ta da sa’i. A qarshe muna addu’ar Allah Ya jikan sa, Ya sa ya huta mu kuma da muke raye Allah Ya sa mu yi kyakkyawan qarshe amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde, Jihar Borno. 09091513043

Ta’aziyyar Prince Audu
Assalamu Alaikum Edita ku ba ni dama in miqa saqon ta’aziyya ga xaukacin al’ummar Jihar Kogi dangane da rasuwar Marigayi Alhaji Prince Abubakar Audu zavavven Gwamnan Jihar Kogi, kuma xan takar jam’iyyar APC. Da fatan Allah Ya jiqansa da rahama, Ya sa kwanciya hutu ce ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannnan babban rashi, mu kuma da muka yi saura idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani amin. Daga Mohammed Maikaset Cross Kauwa Qaramar Hukumar Kukawa Jihar Borno Najeriya. mohammedmaikaset120@yahoo, [email protected] 08138775015.

Kira ga Gwamna Ganduje
Aminiya ku gaya wa Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje ya yi watsi da masu yin maganganun banza, ya sa Jihar Kano gaba, wajen ci gaba da ayyukan da ya gada da kuma wanda zai xora. Masu waxannan maganganu ba aikin ba ne gaban su,  sai dai aljihunsu da ya yi qasa sai su shiga kafafen yax a labarai su yi ta faxar abin da suka ga dama. Daga [email protected]

Kira ga Gwamna Ambode
Salam. Aminiya ina so ku taimake ni ku mika min rokona ga Gwamna Akinwumi Ambode da ya hana barace-barace a Jihar Legas. Domin  yadda darajar Bahaushe take zubewa saboda ’yan uwammu Hausawa da suke zubar mana da mutumci wajen barace-barace. Za ka ga mata da yara kanana suna yawo, ko kuma da jirirai suna nuna bakinsu wai a ba su na abinci. Kuma wallahi har ma cikin shege ake yi musu yanzu. Don Allah  Bahaushe da ke da daraja da kuma addinin Musuunci, ai addini bai ce mata da yara kanana a rika dibarsu ana koya musu yawo zuwa jihohin Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu ba. Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Sha’aibu mile 12 Legas 08111389999, 08096368393

Mu koma ga Allah
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un tabbas ko shakka babu mu al’ummar Arewacin Najeriya muna cikin wani halin da sai dai mu kara dagewa da rokon Allah, tare da gyara tsakanin mu da Allah, ta hanyar istigifari da hailala da salatin Annabi, ko zai kawo mana karshen zubar da jinin bayin Allah. Ganin yadda wasu dauke da boma-bomai suka far wa al’ummar jihohin Adamawa da Kano, inda suka kashe jama’a da dama.  Don haka muke kira ga gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro su dauki matakin ba sani, ba sabo ga duk wanda aka kama da hannu wajen zubar da jinin bayin Allah  da kai hare-haren ta’addanci. A karshe muke rokon Allah Ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya a kasar mu baki dayanta, da ma kasashe makwabtan mu. Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999/ 08138203747 [email protected]   

A kashe wuta lokacin hunturu
Assalam. Edita, lallai yanzu mun shiga lokacin sanyi, mu kula da yara masu hura wuta, don jin dumi da zarar sun gama su kasheta. Haka mutanen kauyuka su ma su sa ido akan duk mai hura wuta don kiyaye gidajensu,wanda mafi yawa kirare ne da manoma suka yi kokarin kwashe amfanin gonakansu, don gudun fataken dare, da aukawar makiyaya gonakinsu. Daga Hussaini Almusaya Gombe, 08130446601

Gargadi ga ’yan majalisa
Aminiya  ’yar amana  don  Allah   ki mika min  sakona  ga  ’yan majalisun  kasa  da su sani  rigar  Shugaba Buhari  suka shiga,  suka ci  zabe,  amma suna nema  su kauce  daga tsarin  da yake so  ya sa kasar nan a gaba.   To,   su sani shekarar 2019  na zuwa,  mu talakawa muna jiransu.  Daga Musa Unguwar Maiyasin  da Rabi’atu  danja Jihar  Katsina 08060611124 08069274090

Ta’aziyya ga Kano da Yola
Assalamu alaikum, Edita ka isar da sakona ga al’ummar Kano da na Yola Jihar Adamawa, bisa rayukan da aka rasa a jihohin dalilin harin bom da aka kai musu,  wanda kungiyar ta’adancin suka kai musu. Allah ya jikan wadanda suka rasu, Ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya.  Daga Bilya Tukur Bakori  09033272527 [email protected]
Ta’aziyyar Prince Audu
Hakika mutuwa rigar kowa. kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina na yin ta’aziya ga iyalai da ’yan uwa da abokan arzika da masoya da Jam’iyar APC da kuma Gwamnatin Jihar Kogi bisa ga rasuwar Prince Abubakar Abdu. Da fatan Allah Ubangiji Ya jikansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Allah Ya sa mu cika da imani. Daga Haruna Muhammad Katsina. [email protected] 07039205659

Jinjina ga jam’iyyar APC
Salam Aminiya  Hausa. Jinjina  ga  jam’iyyar  APC  ta kasa    kan  yin nazari  da zaben da aka  gudanar  a  jihar  Kogi  wanda Allah  ya yi  wa  dan takarar Jam’iyyar  APC  marigayi  Alhaji  Abubakar  Audu rasuwa  da  fatan za su  yi  nazari  bisa  adalci da Gaskiya.  08108003333. [email protected]

Ta’aziyyar Aja Gwarzo
Hakika mutuwa rigar kowa. Muna yin ta’aziya ga iyalai da ’yan’uwa da abokan arzika da Hukumar gidan rediyo Najeriya ta Kaduna (FRCN), bisa ga rasuwar Alhaji Ahmad Aja Gwarzo Mai gabatar da shirin Wasa kwakwalwa da kuma sanarwa.Da fatan Allah Ubangiji Ya jikansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Ya sa mu cika da imani. Daga kungiyar Muryar Jama’a.Reshen Jihar Katsina. 07039205659

Ta’aziyyar Prince Audu
Rai Bakon Duniya.  A yau cikin alhini ina mika sakon ta’aziyyata zuwa ga ‘yan uwa da iyalan marigayi dan takarar gwamnan jihar Kogi wato Alhaji Abubakar Audu.  A gaskiya an yi babban rashi sabili da mutuwa ta yi wa Audu zuwan ba- zata. A bangare guda kuma ina mai jan hankalin ‘yan siyasar Najeriya da su koyi darasi da mutuwar Prince Audu sabili da mutuwa ba ta da sa’i. A karshe muna addu’ar Allah Ya jikan sa, Ya sa ya huta mu kuma da muke raye Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde, Jihar Borno. 09091513043

Ta’aziyyar Prince Audu
Assalamu Alaikum Edita ku ba ni dama in mika sakon ta’aziyya ga daukacin al’ummar Jihar Kogi dangane da rasuwar Marigayi Alhaji Prince Abubakar Audu zababben Gwamnan Jihar Kogi, kuma dan takar jam’iyyar APC. Da fatan Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa kwanciya hutu ce ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannnan babban rashi, mu kuma da muka yi saura idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani amin. Daga Mohammed Maikaset Cross Kauwa karamar Hukumar Kukawa Jihar Borno Najeriya. mohammedmaikaset120@yahoo, [email protected] 08138775015.

Kira ga Gwamna Ganduje
Aminiya ku gaya wa Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje ya yi watsi da masu yin maganganun banza, ya sa Jihar Kano gaba, wajen ci gaba da ayyukan da ya gada da kuma wanda zai dora. Masu wadannan maganganu ba aikin ba ne gaban su,  sai dai aljihunsu da ya yi kasa sai su shiga kafafen yad a labarai su yi ta fadar abin da suka ga dama. Daga [email protected]