Wani masunci a kasar Masar ya tsallake rijiya da baya bayan ya kusa rasa ransa, a yayin da daya daga cikin kifin da ya kama ya makale a cikin makogwaronsa inda ya kai ba ya iya yin numfashi ko kuma ya gaza fitar da kifin daga makogwaron.
A farkon watan nan ne, likitocin sashin kula da marasa lafiya cikin gaggawa na wani asibiti a yankin Beni Suef a kasar Masar suka razana bayan kawo marar lafiyan da yake fuskantar wahalar shakar numfashi lokacin da suka gano cewa kifi ne ya makale masa a makogwaro.
- Tabar wiwi ta sa an tsinka igiyar aure a jihar Oyo
- Harin Bam ya kashe jami’an tsaro 30 a Afghanistan
An gano abin da yake damun masuncin ne bayan binciken likitocin, inda suka tabbatar da cewa, kifi ne ya makale masa a cikin makogwaro da hakan ya sa yake matukar shan wahala wajen yin numfashin.
An gano masuncin yana jan numfashi kadan ne kawai don ya rayu kafin a kai shi asibiti. Jaridar EL-Ain ta Masar ta ce, likitoci sun yi amfani ne da na’ura wajen yi masa tiyata inda suka ciro kifin da ransa.
Wani kwararren likitan kunne da hanci da makogwaro, Dokta Ali Al-Hajri ne ya yi tiyatar ciro kifin daga makogwaron masuncin, kuma likitan ya bayyana wa gidan talabijin din Masar bayan kammala tiyatar cewa mutumin ya yi matukar galabaita.
Sannan an yi nasarar tiyatar, sai dai ya zubar da jini daga cikin makogwaron amma yana cikin koshin lafiya kuma ana fata zai samu cikakkiyar lafiya nan ba da jimawa ba.
Yadda kifin ya shige cikin makogwaron mutumin
Hakan dai ya faru ne da masuncin mai shekara 40 daga kauyen Snur a gabar tekun Nilu, inda ya bayyana wa likitocin cewa, ya kama wani karamin kifi ne sai ya fahimci wani daga cikin kifin da ya kama yana kokarin kubucewa daga cikin komar kamun kifin.
Ya ce a kokarin kama kifi na biyu don kada ya kubuce masa sai ya yi sauri ya saka na farko a cikin bakinsa don ya makale shi da hakoransa, kuma ya yi amfani da hannuwansa wajen kama na biyun.
Sai dai kifin masunci ya rike kifin da hakoransa ne sai kifin a kokarinsa na kubuta daga bakin masuncin sai ya samu hanyar shigewa cikin makogwaronsa a haka ya sulale ya shige da ransa ya makale har zuwa lokacin da aka kai masuncin asibiti.