Wasu yara ’yan makaranta takwas sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwalensu a tafkin Volta da ke Kudu maso Gabashin Ghana.
Yaran sun hadar da maza biyar da mata uku, wadanda shekarunsu suka kama daga biyar zuwa 12.
- An gurfanar da matashi kan satar babura 40 a Ondo
- Take-taken da ake nufi da karancin mai da sauya fasalin Naira —Tinubu
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa yaran sun taso ne daga kauyen Atikagome zuwa garin Wayokope inda makarantar tasu take.
Hukumomin kasar sun ce yaran na daga cikin yara ’yan makaranta 20 da ke cikin kwale-kwalen.
Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala’o’i ta kasar ta ce tuni aka tsamo gawarwakin yaran.
Lamarin dai ya janyo kiraye-kiraye ga gwamnatin kasar da ta inganta harkokin ilimi musamman a yankuna karkara.
A ’yan shekarun baya-bayan nan ana samun yawaitar hatsarin kwale-kwale a kasar, lamarin da ake yawan alakantawa da daukar fasinjoji fiye da kima, da rashin ingancin kwale-kwalen da kuma samun guma-gumai a cikin ruwan.
Ko a watan Afrilun shekarar da ta gabata ma mutum bakwai ne suka mutu a wani makamancin wannan hatsari.