✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kayayyaki sun tashi a Najeriya saboda tsadar farashin mai —NBS

Farashin kayayyaki a Najeriya ya haura zuwa kashi 15.70 cikin 100.

Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya haura zuwa kashi 15.70 cikin 100 a watan Fabrairu, bayan karancin man fetur a cikin gida.

Najeriya ta fara fuskantar karancin man fetur din ne tun a watan Fabrairu wanda har kawo yanzu yake ci gaba da ta’azzara.

Attajirin Duniya yana son dambacewa da Shugaban Rasha kan mamayar Ukraine

Haka kuma hauhawar farashin mai a duniya sakamakon rikicin Rasha da Ukraine ya shafi Najeriya, duk da cewa ta na fitar da danyen mai, amma ta dogara ne kacokan ga man fetur da ake shigowa da shi daga waje.

Karancin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da sufuri, wanda abu ne muhimma ga kasar da ta saba shigo da kayayyaki da ayyuka da dama daga kasashen waje.

Dole sai da kamfanonin jiragen sama suka soke wasu jiragen cikin gida tare da jinkirta wasu a wannan watan da muke ciki na Maris.

Kazalika, karancin dala ya sa gwamnati ta sanya takunkumi kan wasu kayayyaki na musayar kudaden waje, da yanke kayyakin da kuma matsin lamba kan farashin.

Mahukuntan Najeriya sun ce hauhawar farashin kayayyaki da ake ci gaba da fuskanta, yana da nasaba da gibi ba wai kawai ga kudaden da ake samu ba, wanda galibi shigo da su ake yi daga kasashen waje.

A mako mai zuwa ne dai Babban Bankin Najeriya CBN zai yi taro domin kayyade riba.

Ci gaba da hauhawar farashi mai na iya sanadiyyar matsin lamba ga babban bankin kasar da ya sake yin la’akari da matsayinsa game da riba, duk da cewa ci gaban tattalin arzikin yana da rauni.