An gurfanar da wata mata tare da wasu maza uku a gaban wata Kotun Majistare dake Ikeja kan satar kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 26.5.
Mutumin da ake tuhuma mai shekaru 27 da wani mai shekaru 26 da wata mace ‘Yar kasuwa da wani dan shekara 28 da kuma wani mai shekaru 27, dukkansu ana tuhumarsu da kan laifukan da suka hada da hadin baki da sata da kuma karbar kayan sata.
- An gurfanar da matashi kan satar kayan wayar hannu na N1m
- Sarkin Kano ya umarci jama’a su karbi allurar rigakafin coronavirus
Dan sanda mai shigar da kara ASP Clifford Ogu ya shaida wa kotun cewa, mutanen da ake tuhuma sun aikata laifin ne a tsakanin watannin Nuwamba da Disamba na shekarar 2020 a kasuwar Aspamda da ke titin Badagry a birnin Ikko.
Ogu ya bayyana wa Kotun cewa, dukkanin mutanen hudu sun yi tarayya juna wajen halasta kayan haramun.
Dan sandan ya ce laifin da ababen zargin suka aikata ya saba da sashe na 287 da 328 da kuma 411 na kundin dokokin miyagun laifuka na Jihar Legas.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa dukkanin mutanen sun musanta zargin da ake musu na dan hali.
Alkaliyar Kotun, Misis S. K. Matepo, ta bayar da belin mutanen da ake tuhumar kan kudi N100,000 tare da kawo mutune biyu da za su tsaya musu ta kuma dage zaman sauraron shari’ar zuwa 22, ga watan Maris na shekarar 2021.