✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kauyuka biyu aka kaiwa hari a jihar Katsina

Mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata a kauyukan Madobai da Dannakwabo da ke yankin karamar hukumar Kankara bayan da wasu…

Mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata a kauyukan Madobai da Dannakwabo da ke yankin karamar hukumar Kankara bayan da wasu ’yanbindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane suka kai hari a yankin ranar juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da dabbobi da kayan abinci.

Wani daga cikin wadanda harin ya shafa ya ce, “sai da safe muka yi jana’izar wadanda aka kashe bayan an yi masu salla”.

Wannan harin na cikin hare-haren da wannan yanki na Kankara ke fuskanta a wannan lokaci da kullen dakile yaduwar cutar coronavirus ke kara yawaita a jihar ta Katsina.

Haka kuma wannan hari ya zo ne kwana daya da kai hari a garin Mabai wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani manomi mai suna Sada Musa, yayin da Kabiru Muhammad ya samu rauni sanadiyar kwabsar harsashi.

Da farko mutanen kauyen sun yi kokarin kare kansu amma maharani, wadanda yawan su ya haura mutum 70 a kan babura, suka rinjaye su.

Kwanaki hudu da suka wuce wasu ’yan bindiga sun kai hari a makwabtan kauyukan Katsalle, inda aka ce an kashe wasu daga cikin maharan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar harin Mabai, amma ba a samu ko rauni ba a na Katsalle.

SP Gambo Isa ya ce su na nan suna tattara bayanai a kan hare-haren Madobai da Dannakwabi.