✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kauyuka 17 aka kai wa hari a Neja ranar Lahadi

Kananan yara da mata sun rasu a cikin kogi yayin tsere wa ’yan bindiga

Mata da kananan yara sun nutse a ruwa a lokacin da suke kokarin tserewa bayan ’yan bindga sun kai hari a kauyukansu a Jihar Neja.

Gwamnatin Jihar ta ce mutanen sun rasu ne a yayin da suke kokarin tsallaka Kogin Kaduna, a lokacin da ’yan bindiga suka kai hari a kauyuka 17 a Karama Hukumar Wushishi ta Jihar a lokaci guda.

Gwamnatain ta ce mahara a kan babura kusan 70 ne suka kai wa kauyukan farmaki a ranar Lahadi inda suka harbi mutane da dama.

Akalla mutum 10 ne aka kai Babban Asibitin Wushishi  wasu da dama kuma suka bace bayan hare-haren a kauyukan Babako, Tashan Girgi, Kwakwagi, Fakara, Ndiga, Buzu, Akare, Kala Kala, Agwa, Anguwan Gizo, Tsamiya da makwabtansu.

A ranar Lahadin ce kuma ’yan bindiga suka yi awon gaba da daliban Islamiyya kimanin 200 da malamansu a garin Tegina a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar.

An kuma yi garkuwa da fasinjojin wata bas din haya da ke hanyarta ta zuwa Minna, babban birnin Jihar a ranar ta Lahadi.

Amma daga baya Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce ’yan bindiga sun sako 11 daga cikin daliban da suka sace masu kananan shekaru.

Ya bayyana takaici game da karuwar kisan gillar da ’yan bindige suke yi wa mutane a Jihar, amma ya ce rundunar tsaron hadin gwiwa na bin sawun maharan a cikin dazuwa domin gamawa da su.

“Matsalar ta kai ‘intaha’ tamkar ana cikin halin yaki wanda ya kamata a tunkare shi nan take,” inji shi.

Amma ya bukaci mutane da su kwantar da hankali domin gwamnatinsa a tsaye take domin kare rayuka da dukokiyoyinsu, a matsayin babban nauyin da ya rataya a wuyanta.