Makon jiya, mun tsaya daidai inda muke cewa, idan wani ya ce yana tsoron Allah; to lallai babu shakka akwai abin da za mu lura da shi cikin rayuwarsa ta yau da kullum, zai zama mutum ne mai bin dokokin Ubangiji Allah. Babu yadda mutum zai ce yana da tsoron Allah amma kuma ba ya yin biyayya ga maganar Allah. Wani babban masanin Attaurat ya zo wurin Yesu Kristi da tambaya yana so ya gwada shi, sai ya ce da shi “Malam, wacce ce babbar doka a cikin Attaurat? Ya ce masa, ka yi kaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari.”(Matta 22 : 35 -38).
Tambayar da ya kamata mu yi ita ce: Mene ne ma’anar kaunar Allah? Idan muka sake dubawa cikin Littafin Yohanna 14 ; 15, 21-24; Maganar Allah na koya mana cewa, “Idan kuna kaunata ku kiyaye dokokina……..Wanda yake da dokokina, yana kuwa kiyaye su, shi ne yana kaunata, wanda yana kaunana kuwa , za ya zama kaunataccen Ubana, ni ma zan kaunace shi in bayyana kaina gare shi kuma. Yahudi (ba iskariyotiba) ya ce masa: Ubangiji, me ya faru da za ka bayyana kanka gare mu ba ga duniya ba? Yesu ya amsa ya ce masa, idan mutum yana kaunata, za shi kiyaye maganata; Ubana kuwa za ya kaunace shi, mu zo wurinSa mu yi zamanmu tare da Shi. Wanda ba ya kaunata ba, ba za ya kiyaye maganata ba; magana kuwa da kuke ji ba tawa ba ce, amma ta Uba ce wanda Ya aiko ni.”
Abin lura na farko daga inda muka yi karatu shi ne, idan kowane mutum yana so ya nuna kaunarsa ga Allah, akwai abu guda da Allah zai bincika – ko wannan mutum yana yin biyayya ga umurninSa, yin biyayya ga maganar Allah ne kadai abin da ke nuna cewa da gaske ne muna kaunar Allah,babu wata hanya kuma. Wannan biyayyar ba wai dole ne ake sa mutum ba, amma biyayya ne da cikin ra’ayin zuciyarsa ya zaba ya yi, ba abin da ake sa mutum dole ya yi ba ne. sanin maganar Allah na da kyau sosai, amma idan mun sani kawai babu aikatawa; babu yadda za mu ce muna kaunar Allah, akwai masu bi da yawa da suke tsammani za su iya rudin mutane ta wurin yadda suke yin wasu abubuwa kamar nuna kwazo cikin aikin ekklesiyya; amma rayuwarsu a boye abar kyama ce a gaban Ubangiji. Mutane da dama sun haddace maganar Allah a kansu, za ka yi tsammani sun san maganar Allah; amma gaskiyar ita ce sanin maganar Allah a aikata ta ce ba a haddace ta ba, maganar Allah ta ce, “Gama kaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinSa: dokokinSa fa ba su da ban ciwo ba.”(1Yohanna 5 : 3).
Kowane mutum zai iya gwada kansa ya gani ko da gaske ne yana kaunar Allah ta wurin tambayar kansa. Mu binciki kanmu- shin nawa ne daga cikin umarnin Allah da ka sani kuma kake rayuwa bisa ga wannan sani? Za ka iya rudin mutum amma ka sani ba za ka iya rudin Allah Wanda Ya san komai duka ba, ba za ka iya rudin kanka ba domin ka san ko wane ne ne kai.
Wannan kaunar za ta gina ekklisiyar Kiristi: “Domin wannan ina durkusawa a gaban Uba, Wanda kowane iyali cikin sama da duniya ta sami sunanSa daga gare Shi, Shi yarda muku, bisa ga wadatar darajarSa, a karfafa ku da iko ta wurin Ruhunsa cikin mutum na ciki; Kiristi kuma shi zauna cikin zukatanku ta wurin ban-gaskiya: dasassu ne kafaffu kuma cikin kauna, ku karfafa da za ku ruska, tare da dukan tsarkaka, ko mene ne fadi da rata da tsawon da zurfin kaunar Kiristi, ku sani kuma kaunar Kiristi wadda ta wuce gaban a santa, domin ku cika har zuwa dukan cikar Allah.” (Afisawa 3:14 – 19).
Babu yadda ekklisiyar Almasihu za ta ci gaba idan ba mu gane fadin kaunar Allah ba, dole ne mu zama da kauna ga junanmu, domin ta wurin ne kawai za mu iya nuna wa sauran mutane cewa da gaske mu almajiran Yesu Kiristi ne.
Za mu ci gaba da zama cikin Allah: “Idan kuna kaunata kuna kiyaye dokokina; Ni ma in roki Uban, Shi kuma za Ya ba ku wani mai taimako, domin shi zauna tare da ku har abada, shi Ruhu na gaskiya: wanda duniya ba ta iya ta karbe shi ba; gama ba ta ganinsa ba, ba ta kuwa san shi ba: ku kun san shi gama yana zaune tare da ku, za shi kuwa zauna a cikinku. Ba ni barin ku marayu ba; ni zo wurinku, da sauran jimawa kadan tukuna, kana duniya ba za ta kara ganina ba; amma ku kuna ganina: domin ni ina da rai, ku kuma za ku rayu. A cikin wancan rana za ku sani ina cikin Ubana, ku kuma a cikina, ni kuwa a cikinku.” (Yohanna 14:15 – 20).
Mun riga mun ga cewa Allah da kanSa shi kauna ne, haka nan dukan wanda yana tafiya cikin tafarkinSa, idan muka ci gaba da zama cikin irin wannan kauna za mu ci gaba da zama cikin Allah, Ruhun Allah zai ci gaba da zama a cikinmu; Allah ba Ya son kiyayya ko kadan haka bai zai zauna inda akwai kiyayya ba,Yesu Kiristi ya rigaya ya yi mana alkawari cewa ba zai bar mu kamar marayu ba; a kullum zai ci gaba da zama tare da mu har sai ya zo domin shi kai mu wurin kansa.
Za mu zama shaidu ga sauran duniya duka: a cikin Littafin Yohanna 13:34 – 35; maganar Allah na koya mana cewa “Sabuwar doka nake ba ku, ku yi kaunar juna; kamar yadda ni na kaunace ku, kuma ku yi kaunar juna; bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kun da kauna ga junanku.” Abu guda daya da zai bambanta masu bin Yesu Kiristi da sauran mutane na wannan duniya shi ne kAUNA. Yesu Kiristi da kansa ya ce hanya guda daya da mutanen duniya za su fahimta cewa mu almajiransa ne shi ne idan muna da kauna; babu abin da ke iya bayyana halin Allah a fili cikin mutum ko kuwa cikin al’umma fiye da halin kauna ko soyayya a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Muna cikin mawucin zamani da idan mutum bai lura ba, gaskiya, tana da sauki sosai a manta irin wannan kashedin; yau kowa tattali yake yi wa kansa da na kusa da shi, tunanin wadansu daban ma ba ya shiga cikin zuciyarsu balle su ce za su dan taimaka, shi ya sa za ka wanda yake da dan abin hannu, zai ga wanda da gaske ba komai a gidansa da zai sa gaban yaransa, ba domin ba ya son yin aiki ba ne amma domin a gaskiya babu din ne, sai ya ga wannan mai wadatar ya kau da kansa kamar bai gani ba; sai mu tuna da cewa dukan abin da Allah Ya ba mutum AMANA ce daga wurinSa, kuma lokaci na zuwa da kowa zai tsaya a gaban Allah domin shari’a, sai mu yi tunani sosai. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin
kauna (5)
Makon jiya, mun tsaya daidai inda muke cewa, idan wani ya ce yana tsoron Allah; to lallai babu shakka akwai abin da za mu lura…