✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kauna (1)

A yau, za mu soma koyarwa ne a kan wannan muhimmiyar kalma kAUNA. Mutane da dama sun fahimci wannan kalma ta fannoni daban-daban; amma za…

A yau, za mu soma koyarwa ne a kan wannan muhimmiyar kalma kAUNA. Mutane da dama sun fahimci wannan kalma ta fannoni daban-daban; amma za mu yi kokari mu duba abin da Littafi Mai tsarki ke fadi game da irin kaunar da muke so mu yi dan nazari a kai. A yau, za mu soma da karatun ayoyin da suka yi magana a kan kauna kafin mu shiga cikin sassa daban-daban na nazari.
 Mu na Allah ne: wanda ya san Allah Yana jin mu; wanda ba na Allah ba ne ba shi jin mu. Daga wannan mun san ruhun gaskiya mun san kuma ruhun sabo. Masoya, mu yi kaunar junanmu: gama kauna ta Allah ce; dukan wanda yake yin kauna an haife shi daga wurin Allah, ya san Allah kuma. Wanda ba ya yin kauna; ba ya san Allah ba; domin Allah kauna ne. Inda aka bayyana kaunar Allah gare mu ke nan, Allah Ya aike dansa haifaffensa kadai cikin duniya, domin mu rayu ta wurinsa. Nan akwai kauna, ba cewa mu ne muka yi kaunar Allah ba, amma Shi ne Ya kaunace mu, Ya aiki dansa kuma shi zama kafara ta zunubanmu. Masoya, idan Allah Ya kaunaci mu haka nan, ya kamata mu kuma mu yi kaunar junanmu. Ba wanda ya taba duban Allah dadai: idan muna kaunar junanmu, Allah Yana zaune cikinmu, kuma kaunatasa ta cika a cikinmu: haka nan mun sani muna zaune a cikinsa, shi kuma cikinmu, da ya ba mu daga cikin Ruhunsa. Mun duba, kuma mun ba da shaida, Uban ya aike dan shi zama mai ceton duniya. Dukan wanda ya shaida Yesu dan Allah ne, Allah Yana zaune cikinsa, shi kuma cikin Allah. Mun sani, mun gaskanta kuma kauna wadda Allah Yake da ita a wurinmu. Allah kauna ne; kuma wanda yake zaune cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma Yana zaune cikinsa. Haka nan kauna ta cika a wurinmu, da za mu yi gaba gadi kan ranar shari’a; gama kamar yadda shi ke, haka nan muke cikin duniyar nan. Babu tsoro wurin kauna; amma cikakkiyar kauna tana fitar da tsoro, gama tsoro yana da ban wuya, wanda yana jin tsoro kuwa ba ya kammalta wajen kauna ba. Muna kauna domin ya fara kaunatar mu. Idan wani ya ce, ina kamar Allah, shi kuwa yana kin dan uwansa, makaryaci ne shi: domin wanda ba ya yi kaunar dan uwansa ba wanda ya gani, ba shi iya kaunar Allah wanda ba ya gani ba. Kuma muna da wannan umurni daga wurinsa, wanda yake kaunar Allah shi yi kaunar dan uwansa kuma.” (1Yohanna 4:6 – 21). “Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, domin muna kaunar ’yan uwa. Wanda ba ya yi kauna ba cikin mutuwa yake zaune. Inda mun san kauna ke nan, ba da ransa da ya yi dominmu: mu kuma ya kamata mu ba da ranmu domin ’yan uwa. Amma shi wanda yake da dukiyar duniya, yana kuwa ganin dan uwansa da tsiya, ya hana masa tausayi, kaka kaunar Allah tana zaune a cikinsa?  ’Ya’yana kankanana, kada mu yi kauna da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.”(1Yohanna 3:14 -18). “Idan na yi magana da harsunan mutane da na mala’iku, amma ba ni da kauna, na zama jan karfe mai kara,  ko kuwa kuge mai kararrawa. Idan ina da annabci kuma, har kuwa na san dukan asirai da dukan ilimi kuma, idan ina da ban-gaskiya duka kuma har da zan cira duwatsu, amma ba ni da kauna, ni ba komai ba ne. idan ina ba da dukiyata duka domin a ciyar da matalauta, idan kuwa na ba da jikina domin a kone shi, amma ba ni da kauna, ba ya amfane ni komai ba. kauna tana da yawan hakuri, tana da nasiha, kauna ba ta jin kishi; kauna ba ta yin fahariya; ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali; ba ta bida wa kanta, ba ta yin cakuna, ba ta yin nukura; ba ta yin murna cikin rashin yin adalci, amma tana murna da gaskiya; tana jure wa da abu duka, tana gaskanta abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka. kauna ba ta karewa dadai, amma koda zantuttukan annabci, za a kawar da su, ko da harsuna, za su tuke, ko da ilimi, za a kawar da shi. Gama muna sani bisa bisa, muna annabci bisa bisa: amma sa’anda wannan da shike cikakke ya zo, sa’annan za a kawar da wanda shi ke bisa bisa. Sa’anda ina dan yaro, nakan yi magana ta kuruciya, nakan ji kamar mai kuruciya, tunanina na kuruciya ne, amma yanzu da na zama namiji, na kawar da al’amuran kuruciya. Gama yanzu cikin madubi muke gani a zaurance; amma sa’annan fuska da fuska, yanzu na sani bisa bisa; amma sa’annan zan sansance kamar yadda an sansance ni. Yanzu dai ban-gaskiya da bege da kauna sun tabbata, su uku, amma mafi girmansu kauna ce.” (1Korinthyawa:13:1–13). “Kada ku zama mabaratan komai ga kowa, sai dai na kaunar juna: gama wanda ya kaunaci makwabcinsa ya cika shari’a. Gama wannan, Ba za ka yi zina ba, ba za ka yi kisan kai ba, Ba za ka yi sata ba, Ba za ka yi kyashi ba, kuma idan da wata doka, an tarke su cikin wannan magana, cewa , sai ka yi kaunar makwabcinka kamar ranka. kauna ba ta aika mugunta ga makwabcinta ba, kauna fa cikar shari’a ce.” (Romawa13:8–10). “daya kuwa daga cikinsu, wani masanin Attaurat, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce, Malam, wacce ce babbar doka cikin Attaurat? Ya ce masa, ka yi kaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari. Wata kuma ta biyu mai kamanninta ke nan, ka yi kaunar makwabcinka kamar ranka. Ga wadannan doka biyu dukan Attaurat da Annabawa suke ratayawa.”(Matta:22:36–40).
Bisa ga yardar Ubangiji za mu yi bincike kamar haka:

Mine ne kauna?
kaunar Allah ga mutum. Yadda Allah Ya bayyana kaunarsa ga dan Adam
kaunar mutum ga Allah. Yaya za mu san kana kaunar Allah
kaunar mutum ga makwabcinsa. Nuna sahihiyar kauna; da dai sauransu.
Muna cikin mawuyacin lokaci ne a wannan kasar mu Nkjeriya, na lura da yadda mutane suke magana da juna, gaskiyar ita ce sau da dama nakan tambayi kaina cewa – yaya muna zama kamar masu gaba da juna? Yawancin lokaci ba za ka ji kalmomin salama sun fito daga bakin mutane ba; sai ka yi tsammani tamkar muna bakin dagar yaki ne. Mene ne ke kawo irin wannan kiyayya a tsakaninmu? Yaya za a ce muna kasa daya amma akwai gaba a tsakaninmu? Duk wannan na faruwa ne domin rashin kaunar da ke akwai a cikin zuciyar mutane.