✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsina ta kashe fiye da Naira miliyan 10 ga masu matsalar kunne

Ma’aikatar Mata ta Jihar Katsina da hadin gwiwar Gidauniyar Suleiman Ear/Hearing Educational Foundation ta kashe fiye da Naira miliyan 10 wajen taimaka wa marasa galihu…

Ma’aikatar Mata ta Jihar Katsina da hadin gwiwar Gidauniyar Suleiman Ear/Hearing Educational Foundation ta kashe fiye da Naira miliyan 10 wajen taimaka wa marasa galihu da ke da matsalar kunne, inda aka horar da jami’an jinya a matakin farko wadanda suka tunkari matsalar.

Mata da kananan yara 300 da ke da matsalar ciwon kunne a jihar ne suka amfana da shirin.

Da take jawabi wajen bikin mika kayayyakin aikin jinyar kunne ga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina, Kwamishinar Mata ta Jihar, Dokta Badiyya Hassan Mashi, ta ce watanni biyu baya ne aka kaddamar da shirin a asibitin tarayya da ke Katsina, inda aka tantance mutum 400.

Dokta Badiyya Mashi, ta ce masu larurar ji 420 aka tantance inda aka samu 300 da aka yi wa magani aka yi wa mutum 20 aiki a kunne aka bai wa mutum 25 na’urar jin magana, sannan wadansu 5 suna bukatar yi musu aiki nan gaba.

Ta ce gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari ta fi bai wa harkar lafiya kulawa.

Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Mariya Bala Usman, cewa ta yi Gwamnatin Jihar Katsina tana taka rawar gani wajen inganta harkar lafiya a fadin jihar.

Hajiya Mariya wacce Dokta Mukthar Hassan ya wakilta ta kara da cewa duk kokarin gwamnati dole sai an samu kungiyoyi sun taimaka kamar yadda Gidauniyar Suleiman ta yi yanzu.

Shugaban Gidauniyar Suleiman, Dokta Suleiman Abdulmajid, ya ce sun fara tantancewar ce a ranakun 11 zuwa 17 ga watan Oktoba. Ya ce wadansu da suka bai wa magani datti ne ya toshe musu kunne ba ciwon da sai an yi musu aiki ba, amma ba a sani ba sai da suka duba suka gani.

An horar da jami’an lafiya bibiyu ne a cibiyoyi 3 da ke mazabun dan Majalisar Dattawa  a jihar da za su gudanar da aiki a asibitocinsu.