✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Katsina: An sace matar tsohon shugaban PDP a Batsari

Har yanzu ba a san adadin mutanen da aka kwashe ba

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane da dama, cikinsu har da matar tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Batsari da ke jihar Katsina, Hurera Salisu Mai Maganin Kwari.

Alhaji Salisu dai yanzu daya ne daga cikin kusoshin jam’iyyar a jihar.

An sace matar ce tare da wani malamin makaranta mai suna Lurwanu Batsari da diyar wani dan sanda mai suna Ya’u Lumbari tare wasu mutanen da har yanzu ba a san yawan su ba.

’Yan bindigar sun tsare hanyar Katsina zuwa Batsari ne da yammacin Asabar a daidai garin Dutsin Kura, inda suka yi awon gaba da wadannan mutane zuwa daji.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce, har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai samu wani bayani daga DPO na yankin ba a kan harin.

Sai dai ya yi alkawarin sanar da wakilinmu da zarar ya samu cikakken bayani.