✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katse lantarkin Najeriya: NLC da kamfanin TCN sun sa zare

NLC ta karyata zargin da TCN ya yi wa jami'an kungiyar na dukan ma'aikata a tashoshin lantarki

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta zargi Kamfanin Wutar Lantarki na Kasa (TCN) da amfani da sojoji wajen tursasa wa ma’aikatansa yin aiki a yayin yajin aikin gama-gari da kungiyar ke gudanarwa.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya gargadi TCN cewa ya shirya daukar alhakin duk abin da ya sami mambobinta a hannun sojojin da ke musu karfa-karfa.

Ajaero kuma karyata zargin da TCN ya yi cewa mambobinta na lakada wa ma’aikatansa duka har suka jikkata su a lokacin da suke bakin aiki a tashoshin lantarki.

A safiyar Litinin TCN ta fitar da sanarwa, dauke da sa hannun Ndidi Mbah, cewa jami’an NLC masu dabbaka umarnin yajin aiki sun yi dirar mikiya a wasu tashoshinsa, inda suka lakada wa ma’aikatan duka suka jikkata wasu sannan suka kaste babban layin wutar kasar.

NLC ta bayyana zargin da cewa karya ce tsagwaronta, da kuma neman goga wa kungiyar kashin kaji.

A cewarta, babu inda jami’an NLC suka ci zarafin wani ma’aikaci ballantana har su yi masa rauni.

Ta zargi TCN da neman amfani da yajin aikin wajen daukar Dala babu gammo alhali ba kamfanin kadai yajin aikin ya durkusar da harkokinsa ba a Najeriya.

Kungiyar ta kara da cewa ya kamata kamfanin ya sani cewa ’yancin ma’aikata ne su shiga yajin aikin, kuma dole idan suka shiga ayyuka su tsaya domin babu wanda zai sarrafa injina.

Don haka ta yi mamakin dalilin da kamfanin ke neman nuba bai san hakan ba.

Sanarwar martani da NLC ta fitar ta ce kamata ya yi tun farko TCN ya sani cewa kafin fara yajin aikin sai da kungiyar ta ba gwamnati isasshen wa’adi domin kara mafi karancin albashi da kuma soke karin farashin wutar lantarki.

Sanarwar dauke da sa hannun Shugaban NLC na Kasa, Kwamred Joe Ajaero, ta ce kamata ya tun lokacin kamfanin ya sa baki domin gwamnati ta yi abin da ya kamata domin jin dadin ma’aikata, ba ya bari sai an fara yajin aikin ya dawo yana fargar jaji ba.