A ranar Talatar da ta gabata ce kasar Katar ta ba da sanarwar yanke shawarar janyewa daga cikin Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC).
Sanawar ta ba-zata da Ministan Makamashi na Katar, Sa’ad Sherida al-Ka’abi ya bayyana, na nuni da cewa, kasar na son cimma burinta na kara yawan danyen man da take hakowa a kullum, domin karfafa tattalin arzikinta da ke fuskantar kalubale dalilin yanke hulda da Saudiyya ta yi da ita, tare da goyon bayan kasashen Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Baharain.
Wannan shi ne karo na farko, da wata kasa ta yankin Gabas ta Tsakiya ke ficewa daga cikin Kungiyar OPEC, wadda aka kafa a 1960.
Yayin sanar da daukar matakin, Minista al-Ka’abi ya ce kasar za ta kara yawan danyen man da take hakowa daga ganga miliyan 4 da dubu 800 a rana zuwa ganga miliyan 6 da rabi.
A bangaren Iskar Gas kuwa, Ministan ya ce Katar za ta kara yawan wadda take hakowa daga tan miliyan 77 a kowace shekara zuwa tan miliyan 110.