✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar Panteka ta Kaduna ta samu lasisin koyar da sana’o’i —NBTE

Da takardar shaidar NSQ wadanda suka kammala koyon aiki a kasuwar Panteka za su iya samun aiki a kowane matakin gwamnati da ma a kasashen…

Hukumar Sa Ido kan Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE) ta bai wa tsohuwar Kasuwar Panteka da ke Kaduna lasisin zama Cikakkiyar Cibiyar Horas da Ilimin Kere-kere. 

Babban Sakataren Hukumar NBTE, Farfesa Idris Muhammad Bugaje, ya ce “A kwai sama da mutane dubu 38 da ke koyon sana’o’i iri daban-daban a wannan kasuwa ta tsohuwar Panteka”.

Da yake jawabi a kasuwar ranar Litinin, Farfesa Bugaje ya bukaci shugabannin kasuwar su nemi lasisin koyarwa daga hukumarsa, domin wadanda ke koyon aiki a wurinsu su rika samun takardar shaidar kwarewa da gwamnati ta aminta da ita.

Ya bayyana cewa tun a shekarar 2021 kasuwar ta kulla alaka da Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna domin saukaka yadda ake koyar da sana’o’i a kasuwar, inda “wasu daga cikin daliban suka kammala karatunsu a watan Nuwamba 2023.”

Bugaje ya kara da cewa, a yanzu an shigar da wani tsari na masu sana’ar hannu da ake wa lakabi da NSQ a cikin tsarin ayyuka a Najeriya.

Ya ce da takardar shaidar NSQ wadanda suka kammala koyon aiki a kasuwar Panteka za su iya samun aiki a kowane mataki na gwamnati da ma ayyukan yi a kasashen waje.

Farfesa Bugaje ya kara da cewa da gudummawar da hukumar TETFUnd ke bayarwa da kuma agajin Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna da kuma abin da gwamnatin jihar ke yi wa kasuwar a yanzu, babu shakka ana iya cimma hakan.

Bugaje ya ce, Panteka itace cibiyar kere-kere na zamani mafi girma a Afirka, domin makamantanta da ke Kenya da Tanzaniya, da ake kira ‘Jua Kali,’ ba su kai ta yawan masu koyon aiki ba.

A nasa jawabin, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce Kasuwar Panteka da aka gyara tare da samar da kayan aiki na zamani da hanyoyin shiga za su jawo hankalin jama’a daga sauran jihohi da kuma bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

“Ba wai kawai muna gyara kasuwar ba ne, muna kara wasu gine-ginen da ake da su wadanda za su mayar da kasuwar cikakkiyar cibiyar kasuwanci da fasaha,” in ji shi.

Uba Sani ya ce kasuwar da aka inganta a yanzu za ta samu asibiti, tashar kashe gobara, bandakuna, injinan samar da wuta, ofisoshin jami’an tsaro, wuraren ibada, da kuma cibiyar fasahar zamani ICT.

Gwamnan ya kara da cewa za a horar da matasa sana’o’in kafinta, walda, zane-zanen gidaje da aikin famfo, aikin lantarki, da ma wasu sana’o’i masu amfani a al’umma.

An gyara kasuwar ce bayan wata gobara da ta lakume dukiyoyi da shaguna sama da 200 a shararriyar kasuwar da ke makwabtaka da da Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna.