✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwanci ba na maza kadai ba ne – Hajiya Farida Musa Kalla

Hajiya Farida Musa Kalla ita ce Shugabar Kamfanin FMK da ke Kano wanda ke harkokin sayar da atamfofi da yadi da sauransu. A tattaunawarta da…

Hajiya Farida Musa Kalla ita ce Shugabar Kamfanin FMK da ke Kano wanda ke harkokin sayar da atamfofi da yadi da sauransu. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa kasuwanci ba na maza kadai ba ne, mata ma akwai irin rawar da za su iya takawa a fagen:

Tarihin rayuwa

An haife ni a Unguwar Gwammaja a birnin Kano. Na yi firamare a makarantar  Special Model daga nan na tafi Makarantar Sakandaren St. Louise  sai dai na karasa karatuna a Makarantar Sakandaren Cresent. Bayan na kammala sai na samu gurbin karatu kan aikin banki a Jami’ar Bayero inda na samu shaidar Diploma. Bayan na kammala sai na yi karatun Digiri a bangaren tsimi da tanadi (Economics) a Jami’ar Bayero. Ina cikin wannan karatu ne na yi aure. Bayan na kammala sai na yi aikin hidimar kasa a Asibitin Kashi na Kasa da ke Dala a bangaren harkar kudi.

Yadda na fara  kasuwanci

Zan iya cewa kasuwanci ba shi ne abin da na yi burin yi ba, domin ina makaranta burina shi ne in yi karatu mai zurfi in yi aikin gwamnati. Amma cikin ikon Allah bayan na yi aure sai maigidana da yake shi dan kasuwa ne, sai ya sanya ni a harkar. Ba na mantawa a lokacin da nake hidimar kasa a Asibitin Kashi sai maigidana ya ba ni wasu mayafai ya ce in rika sayarwa. Da yake Allah Ya sa ina da rabo a harkar ina farawa sai abin ya samu karbuwa. Da na ga haka sai na je na sayi wasu atamfofi guda 100 na ajiye su na fara sayarwa. Ba a yi wata uku ba atamfar nan ta kare. Hakan ya ba ni kwarin gwiwa na dauki kudina Naira dubu 600 da mahaifiyata ta ba ni da niyyar in sayi mota a lokacin da nake karatu. A ganinta ina shan wahala ga shi na fara haihuwa ga kuma zirga-zirgar karatu. To a lokaci sai maigidana ya ki amincewa in sayi mota inda ya nuna cewa shi ne ya kamata ya saya min mota amma ba iyayena ba, don haka a cewarsa sai dai in ajiye kudina in yi wani abin da su.

To da na fara kasuwancin sai ya shawarce ni in yi amfani da wannan kudi inda ya sa aka kawo min wata atamfa daga Indiya ganin yawan kayan ya sa maigidana ya fara shakkun yadda cinikin zai kasance, amma cikin ikon Allah nan ma sai ga shi sai kudina. Tun daga wannan lokaci sai abubuwa suka rika bunkasa har ya kai na bude shago a cikin gidana. Ya zama ina bayar da oda a yi min kaya nawa na kaina a kasashe daban-daban tare da raba wa ’yan kasuwa maimakon karbar kaya da nake yi a wajen ’yan kasuwar. A yanzu dai alhamdulillah domin  ta kai ina da shaguna guda uku a cikin Kasuwar Kantin Kwari. A yanzu haka ma muna  kokarin bude wani shagon nan ba da dadewa ba.

Nasarori

Zan iya cewa alhamdulillahi saboda shi kansa bude shagunan ma nasara ce. Bayan haka kuma ina da ma’aikata wadanda ke aiki a karkashina sama da 22 da nake biyansu albashi duk wata. Wani abu da ke kara sa ni farin ciki shi ne yadda nake biyan albashin ba tare da wani bacin rai ba. Wallahi duk lokacin da zan biya ma’aikatana na fi su farin ciki saboda ina ganin Allah Ya yi min baiwar da wani zai  nemi abinci a karkashina.

Kalubale

A rayuwa ko me mutum yake yi ba ya rasa kalubale. amma ni ina godiya ga Allah bisa yadda abubuwa suke zuwa min da sauki. Kin ga ko batun kula da gida ban samu matsala ba. Domin ina da ma’aikata da ke taimaka min. Kuma maigidana yana da fahimta. Hakikanin gaskiya ma shi ne yake ba ni kwarin gwiwa a kan harkokina. Haka kuma batun gudanar da harkaokina alhamdulilah ina gamsuwa game da yadda al’amuran ke tafiya. Sai dai ta bangaren kaya za ki ga wasu lokutan kina fama da mutane wajen biyan kudi.

Farida Musa Kalla da ’ya’yanta
Farida Musa Kalla da ’ya’yanta

Iyali

Ina tare da maigidana Alhaji Saminu. Allah Ya albarkace mu da ’ya’ya hudu amma daya ta rasu. Yanzu akwai Sayyad sai Fatima da kuma Huda.

Burina

Ina burin in ga kasarmu ta ci gaba kamar yadda sauran kasashe suka ci gaba musamman ta fuskar masana’antu. Za ki ga cewa a yanzu a kasar nan ba mu da masana’antun da za su iya yi mana ko fitar mana da zanen atamfa ko yadi. Duk lokacin da muka bayar da odar kaya sai dai mu tura su yi mana zane sannan a turo da shi a gani sannan mu sake turawa a fitar da launika irin wadannan abubuwa ne da za a iya yin su a kasar nan ba tare da an fita kasar waje ba. Amma saboda matsalolin kasar nan mun kasa kaiwa wannan matsayi. Muna da matsalar rashin wutar lantarki da rashin taimakawa daga bangaren gwamnati.

Abin da nake so bari bayana

Babban abin da nake so in bari a bayana shi ne in ga ’ya’yana sun samu kyakkyawar tarbiyya wacce kowa zai yi sha’awarsu, ta yadda ko bayan raina idan aka gansu za a tuna da ni a matsayin wacce ta ba ’ya’yanta tarbiyya wanda kuma hakan zai amfani al’umma.

Mutanen da nake koyi da su

Ba ni da abin koyi  kamar mahaifiyata

Shawarata ga mata

Ina shawartar ’yan uwana mata su zama masu dogaro da kansu. Mata su mike su nemi sana’a. Muna cikin wani zamani da dole sai mace ta nemi nata sannan rayuwar aurenta take inganta. Ko ba komai mace mai sana’a ita ke tallafar rayuwar ’ya’yanta. A wannan zamani ma maza ba su son macen da ba ta da sana’a domin su ma sauki suke nema lura da yadda yanayin tattalin arzikin kasa yake. Ita kuma sana’a ba a fara yin ta da tsoro, idan kika yi shawarar za ki fara sayar da abu kaza to kawai ki fara gwadawa. Idan ba ki ga daidai a farko ba kada ki bari hakan ya sanyaya miki gwiwa. Ki ci gaba da jarrabawa har Allah Ya sa ki ga ribar abin. Abin da ake bukata shi ne jajircewa da hakuri har wata rana a kai ga rabo.

Haka kuma mata su ajiye batun kawaye a gefe. Ba a ce mace ba za ta yi kawa ba, amma yadda mata suke ba kawa muhimmanci abin akwai damuwa kwarai. Za ki ga wadansu matan kawayensu ne ke tafiyar musu da ragamar gidajensu domin babu abin da zai gudana a gidan ba tare da ta nemi shawarar kawa ba. Ni ina ganin rayuwar gidan aure kamar makaranta ce idan kika yi shekarar farko, kika kara ta biyu za ki ga kin samu ilimin yadda za ki ci gaba da gyara zamantakewarki da mijinki. Amma ba wai ki dogara kacokan kan kawarki ko wata aminiyarki ta rika ba ki shawara a kan gidanki ba. Wannan ba daidai ba ne. Kuma da mun duba da yawa kawayen nan su ne ke rusa rayuwar gidajen kawayensu. To kamata ya yi ki dogara da kanki wajen samo mafita gare ki amma ba ta hanyar bin kawaye ba.