Wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Jihar Kaduna da aka kama ya ce yana rokon a yafe masa.
Mutmin da aka kama, mai shekara 47, wanda ya addabi yankin Rigachikun a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, ya ce shi tsohon dan kasuwa ne, amma yana rokon a yafe masa, ba zai sake ayyukan ta’addanci ba.
- Taliban ta haramta aske gemu da jin kida a Afghanistan
- Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a Yobe
“Na yi alkawari wannan shi ne na farko kuma na karshe, na yi alkawari ba zan sake taba kayan wani ba; Ina roko a tausaya, a yafe min ba zan sake garkuwa da mutane ba,” inji shi, bayan ya shiga hannu.
– ‘Wuraren da muka yi garkuwa da mutane’
Ya kuma bayyana sunayen mutanen da ya yi garkuwa da su, da kudin fansar da aka biya.
“Mun sace wani mai suna Abdul, aka biya kudin fansa N200,000, Alhaji Umaru ya biya N500,000, Alhaji Birau kuma miliyan uku, sai Alhaji Ibrahim N700,000”, inji shi da yake lissafa mutanen da ya yi garkuwa da su.
Ya ce akwai kuma masu garkuwa a yankin Maraban Jos inda ya ce, “Lawal Isah, Awalu, Bature Goma, Gamji, Sule da suransu ne suke yankin, inda suka yi garkuwa da mutane aka ba su kudin fansa Naira miliyan 10; Sun kuma kashe wata mata, kamar yadda muka ji.”
“Akwai kuma Yusuf, Sale, Gomi, Nasiru, Tukur, Banki, Magaji sannan a yankin Kurama kuma su Musa ne da Kadi, Oriya, Ibrahim, Bala, Rabo, Gaya, Malan, Usama, Babangida, Abubakar, Sule, sai dayan, na manta sunasan; Amma shi daga baya ya koma wurinsu Babangida, Suleiman da Sule”.