Kasurgumin dan bindigar nan da aka fi sani da Dogo Gide, ya haramta sayarwa ko shan miyagun kwayoyi a wasu kauyukan masarautar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Aminiya ta gano cewa Dogo Gide, wanda yake da sansani a dajin Kuyambana ya addabi Jihohin Zamfara da Kaduna da Neja da kuma Kebbi.
- Abduljabbar ya nemi kotu ta ba shi damar kare kansa ba tare da lauyoyi ba
- An yi wa Fursunonin Najeriya karin kudin abinci
Ko a farkon makon nan sai da rahotanni suka tabbatar da yadda wata arangamar yaransa da na Damina, wanda shi ma wani kasurgumin dan bindiga a yankin, ta yi sanadiyyar mutuwar Daminan.
Dogo Gide dai ya gargadi mazauna yankin Babbar Doka inda ya shafe kusan shekara biyar yana iko da shi, cewa dukkan wanda aka kama yana ta’ammali da kwayoyi za a kashe shi a bainar jama’a.
Wata majiya a yankin ta shaida wa wakilin Aminiya cewa tun da farko dai Dogo Giden ya taba kwace wasu kwayoyin daga wasu da ake zargin dilolinsu ne, sannan ya banka musu wuta.
Daga nan ne kuma ya kiyasta kudin kwayoyin sannan ya biya wadanda suka yi safararsu, tare da gargadin yaransa dasu kaurace musu.
“Wani harin da wasu da sojoji suka kai wa wasu da ake zargin masu ba ’yan bidniga bayanai ne a yankin Dansadau ya kai ga kama wasu dilolin kwayoyi, ciki har da wani mai suna Zakin Goro.
“A wasu lokutan, ’yan bindigar kan sayi wata kwayar magani mai suna Pentazocine da kuma Tramadol,” inji majiyar.
Ana dai amafani da maganin ne domin rage radadin ciwo, musamman ga marasa lafiyan da aka yi wa tiyata, inda su kuma ’yan bindigar ke amfani da ita don su bugu.