✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KASUPDA ta hana yin Sallar Juma’a a Masallacin ASD

A ranar Juma’ar da ta gabata ce gwamnatin Jihar Kaduna ta hana yin Sallar Juma’a a sabon masallacin da Alhaji Sani Dauda (ASD) ya bude…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce gwamnatin Jihar Kaduna ta hana yin Sallar Juma’a a sabon masallacin da Alhaji Sani Dauda (ASD) ya bude a gidansa da ke Titin Yakubu Abenue a Kaduna.

A cewar Hukumar Kula da Tsare-tsaren Birnin Kaduna (KASUPDA) da ke da alhakin ba da lasisin yin gini a jihar an hana yin Sallar Juma’ar ce kawai saboda  ba masallacin Juma’a aka nemi ginawa tun farko a wajen ba.

Aminiya ta gano cewa an bude sabon masallacin ne a makon jiya wanda dan kasuwa Alhaji Sani Dauda (Mai Kamfanin ASD Motors) ya gina.

Mutane da dama ne suka halarci bikin bude sabon masallacin wanda aka hada shi da daurin auren ’yar ASD da dan Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato a ranar.

Amma sai daga bisani gwamnatin jihar ta hannun Hukumar KASUPDA ta ce tun farko lasisin gyaran karamin masallacin da ke wajen suka nema ba na masallacin Juma’a ba.

Da take bayani ga Aminiya a ofishinta Shugabar Hukumar KASUPDA Malama  Fausat Ibikunle ta ce ba su hana yin salloli biyar a masallacin ba, amma ba za a yarda a rika yin Sallar Juma’a ba domin lasisin da aka ba su ba na Masallacin Juma’a ba ne.

Ta ce akwai wurare na musamman da aka amince a gina  masallatan Juma’a amma ba a tsakiyar gidajen mutane ba.

“Lokacin da suka zo neman lasisin gyara karamin masallacin da ke gidan an ba su, amma daga baya sai muka rika ganin hotuna a kafafen sada zumunta cewa  za a bude Masallacin Juma’a a wajen.

Ganin haka ni da kaina na je wajen na duba sai na ga ashe masallacin da suka ce za su gyara ne amma dai mu ba lasisin Masallacin Juma’a muka ba su ba. Wannan ya sa muka sake rubuta musu wasika  cewa gaskiya  ba abin da suka ce za su yi ba ne suka yi don haka ba za a amince da shi ba,” inji ta.

“Amma dai abin da nake son kowa ya sani shi ne a matsayinmu na hukuma ko gwamnati ba mu da matsala da bude masallaci sai dai akwai bukatar a rika bin ka’idoji saboda haka wannan masallaci lasisin da aka bayar ba na Sallar Juma’a ba ne, “ inji ta

Wakilin Aminiya wanda ya ziyarci masallacin ya ce a ranar Juma’a an kulle masallacin sannan  ya ga ’yan sanda a wajen rike da makamai.

Kokarin jin ta bakin wanda ya gina masallacin Alhaji Sani Dauda ya ci tura domin bai amsa waya ko sakon tes da wakilinmu ya aike ba masa a kan batun.

Amma dai wakilinmu ya samu labari daga wajen wata majiya cewa  wadansu manyan malaman Musulunci sun ziyarci Gwamna El’Rufa’i a kan batun amma ya ce tunda ba a bi ka’ida ba, shi ba zai iya yin wani abu a kai ba.