Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta musanta cewar an kulle jami’ar saboda zanga-zangar da dalibanta suka yi kan karin kudin makarantar.
Kakakin jami’ar, Adamu Nuhu Bargo, ya musanta labarin rufe makarantar da ke yawo a kafafen sada zumunta ta wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- Nan gaba kadan za a yi bayani kan Hajjin 2021
- Janar 29 za su tafi hutun barin aiki bayan nada Farouk Babban Hafsa
“Hukumar Gudanarwar Jami’ar KASU na sanar da ma’aikata, dalibai da sauran jama’a cewa babu gaskiya a labaran da ke yawo cewa an rufe jami’ar.
“Ana yada labarin karyar ne don dakile ci gaban harkokin jami’ar, saboda haka muke kira ga jama’a da su ci gaba da harkokinsu yadda suka saba,” inji shi.
Aminiya ta gano an kulle kofar shiga jami’ar a ranar Litinin, aka kuma hana dalibai shiga cikinta.
Wakilinmu ya ziyarci jami’ar ta KASU da yammacin ranar, don gane wa idonsa halin da ake ciki, inda ya iske mutane kalilan a cikinta suna kai-komo.
Wata daliba da ta bukaci a boye sunanta ta ce, “An hana dalibai shiga cikin makarantar, mun kuma samu labarin cewar hukumar gudanarwa ce ta ba da umarnin a rufe”.
Aminiya ta ruwaito yadda daruruwan daliban jami’ar suka gudanar da zanga-zanga a makon jiya kan karin kudin makarantar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a baya-bayan nan.
A yayin zanga-zangar, dandazon daliban sun tare titin zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, don nuna fushinsu kan karin kudin makarantar da gwamnatin ta yi.