Shugaban Kwamitin Bankuna da Inshora na Majalisar Dattijai, Sanata Uba Sani, ya ce kimanin kaso 60 cikin 100 na mutanen Arewacin Najeriya ba su da asusun ajiya na banki.
Ya ce alkaluman sun bambanta da na Kudancin kasar inda kaso 80 na mutane ke da asusun ajiyar.
- Elon Musk ya dawo wa Donald Trump shafinsa da Twitter ta dakatar a baya
- Matsalar wutar Lantarki: Ganduje zai yi rusau a Kano
Uba Sani, wanda kuma shi ne dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da Sashen Hausa na BBC da safiyar Litinin.
Ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya da shugabannin addinin da ’yan kasuwa da ’yan siyasa da su tashi tsaye wajen ganin sun kawo sauyi a lamarin.
A cewar Sanatan, akwai tsare-tsaren basuka da tallafin gwamnati da mutanen yankin da dama ba sa amfana da su, saboda yadda suka tsani kudin ruwa da rashin son bude asusun.
Ya ce hatta kananan bankuna (na Microfinance) da ke Arewa, ’yan Kudu ne suka mallake su.
“Yayin da kaso 80 cikin 100 na ’yan Kudu suna da asusun ajiya na banki, ya kamata masu hannu da shuninmu su kafa nasu bankunan saboda yanzu haka kaso 80 cikin 100 na kanana bankunan da ke Arewa ma mallakin ’yan Kudu ne.
“Dole ne masu kudinmu su karkafa bankuna a yankin idan suna son su ci gaba,” inji shi.
Ya ce akwai malaman addinin Musuluncin da suka yi rubuce-rubuce a kan yadda mutum zai karbi bashi ba tare da kudin ruwa ba, kuma an samu sauye-sauye a kan haka.