Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya ce ’yan Afirka a yanzu na cinye kusan kaso 40 cikin 100 na kudin shigarsu a abinci kawai.
Shugaban ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na Bankin Raya Kasashen Afirka, da Shugabannin Kasashe, da Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a Accra da ke kasar ta Ghana.
- ‘A taimaka a ceto mana ’yan uwa daga hannun ’yan bindiga’
- ’Yan bindiga sun harbe manoma 15 a Katsina
Ya ce wannan kaso ya haura sosai idan aka kwatanta da kaso 20 da kasashen da suka ci gaba ke kashewa a gidajensu.
Akufo-Addo ya alakanta hauhawar farashin kayan abincin da ake fama da shi sa yakin Rasha da Ukraine, wanda ya ce ya taba bangarorin tattalin arzikin kasashe da dama.
“Tun a watan Fabrairun 2022, farashin kayayyakin masarufi ya tashi sosai, kasuwanni na kara tsiyacewa, wanda hakan ba karamin shafar iyalai da dukiyar al’umma ya yi ba.
“Kazalika wannan matsala na neman kassara yankinmu na Afirka, domin idan aka yi la’akari da kididdigar da UNECA ta fitar, annobar Kwarona ta sanya an samu karin karbar bashin kudaden shiga daga kaso 60 zuwa 71.1 cikin 100 tun daga shekara ta 2019 har zuwa 2020,” inji Shugaban.
Ya kara da cewa a yanzu gudummawa ga kasashen da ba sa kan tsarin Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) domin rage basukan da ke kansu takaitacciya ce.