✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 70 na ’yan Najeriya da aka bai wa cin hanci a shekarar 2023 sun ƙi karɓa — ICPC

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC a Nijeriya, ta ce kashe 70 na wasu jama’ar ƙasar da aka bai wa cin hanci…

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC a Nijeriya, ta ce kashe 70 na wasu jama’ar ƙasar da aka bai wa cin hanci a shekarar 2023 da ta gabata sun ƙi karɓa.

Shugaban Hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu, ya bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nijeriya da aka bai wa cin hanci aƙalla ko da sau ɗaya ne a bara sun ƙi karɓa.

Shugaban ya yi wannan bayani ne a yayin taron lauyoyi da aka gudanar a Jihar Kano domin haɗa kai wajen ƙarfafa matakan yaƙi da rashawa.

Shugaban ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma ne ya fi rinjayen alƙaluman mutanen da suka ƙi bayar da cin hancin, inda ya ce wannan ya nuna ƙaruwar rashin yarda da cin hanci a yankin.

A bayan nan ne ICPC ta ce cin hanci ya durƙusar da Nijeriya tare da gurgunta ci gaban tattalin arziki ƙasar.

Hukumar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance jajirtattu wajen fallasa ayyukan cin hanci da rashawa da kuma yaƙi da matsalar da ra bayyana a matsayin annoba.