✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 59 na mata na fuskantar cin zarafi a Gombe – Matar Gwamna

Uwargidan ta ce dole ne masu ruwa da tsaki su haɗa hannu domin kawo ƙarshen cin zarafin mata da ƙananan yara a jihar.

Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammad Inuwa Yahaya, ta bayyana cewa kashi 59.3 cikin 100 na mata a jihar, sun taɓa fuskantar nau’in cin zarafi.

Ta bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Yaƙin Kwana 16 na fadakarwa game da cin zarafin mata da ƙananan yara a jihar.

“Ƙididdiga ta nuna cewa kashi ɗaya cikin uku mata a duniya na fuskantar cin zarafi.

“Wannan abu ne da ba za a amince da shi ba, dole ne mu haɗa kai domin kawo ƙarshensa,” in ji ta.

Ta kuma jaddada cewa gangamin na da nufin wayar da kai, ƙarfafa fafutuka, da kuma haɗa kan al’umma don kawo ƙarshen cin zarafin ’ya’ya mata.

Ta buƙaci haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu, ƙungiyoyin kare haƙƙin matada sauran masu ruwa da tsaki don samun nasara.

A nata jawabin, Kwamishinar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar, Asma’u Muhammad Iganus, ta tabbatar da ƙudirin gwamnati na kawar da duk wani nau’in cin zarafin mata.

Har ila yau, ta bayyana cewa yaƙin na bana, wanda aka fara a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2024, zai ƙare a ranar 10 ga watan Disamba, 2024.

Ta ƙara da cewa an samu gagarumin ci gaba ƙarƙashin gwamnatin Muhammad Inuwa Yahaya, musamman wajen samar da dokokin da za su kare masu rauni.

Kwamishinar ta yaba wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, bisa jajircewarsa wajen ganin an zartas da muhimman dokoki da suka shafi kare haƙƙin masu rauni a lokacinsa.

Ta kuma yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su haɗa kai da matansu wajen kafa kwamitocin kare haƙƙin yara a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu.