✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kashi 10 na masu shan miyagun kwayoyi a Najeriya ‘yan Kaduna ne – NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ta ce daga cikin  mutane miliyan 14.3 da ke shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya, akalla kashi 10…

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ta ce daga cikin  mutane miliyan 14.3 da ke shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya, akalla kashi 10 daga ciki mazauna jihar Kaduna ne.

Shugaban sashen binciken sirri na hukumar reshen jihar, Abdulrazaq Umar muammad, ne ya bayyana hakan, a wani taron wayar da kai da Kungiyar Likitoci masu ba da Magungunan Musuluinci (IMPAN) ta shirya a jihar.

Ya ce ako a baya-bayan nan sai da hukumar ta kwace kwalabe 26,000 na maganin Kodin a Kadunan, in da ya ce hakan ya faru ne sakamakon jihar ta zamo tashar shige da ficen miyagun kwayoyin a arewacin Najeriya.

Kazalika ya ce mutane miliyan uku daga cikin wancan adadin, da mafi yawansu matasa ne da mata da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya, ta zame musu jiki.

A nasa jawabin wakilin Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC),  Shamsudeen Mani, ya bukaci kungiyar ta IMPAN da ta wayar da kan ‘ya’yanta kan muhimmancin yin rijistar kamfanoninsu da hukumomin da abin ya shafa.

Shi ma dai shugaban kungiyar ta IMPAN reshen jihar, Tijjani Alsari, ya ce kungiyar a shirye take ta bi dukkanin dokoki da ka’idojin da dukkanin hukumomin gwamnati a kasar nan suka shimfida.