✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe malamai ba zai hana addini ci gaba ba (3)

An karbo Hadisi daga Abu Sa’id Al-Khudriy (RA), ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kada kwarjinin mutane da tsoronsu ya hana mutum fadar gaskiya…

An karbo Hadisi daga Abu Sa’id Al-Khudriy (RA), ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kada kwarjinin mutane da tsoronsu ya hana mutum fadar gaskiya idan ya san ta.” Hadisi ne ingantacce, Tirmiziy ya ce Hadisi ne mai kyau. Al-Imam Ibnu Majah da Al-Hakim da Ahmad duk sun fitar da Hadisin. Kuma Muhammad Nasiruddin Al-Albani ya kawo shi a As-Saheehah, Lamba na 168. Kuma Al-Imamu Baihaki ya fitar da Hadisi a Shu’ubul Iman da Isnadi mai kyau, daga Abdullahi dan Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba ya kamata ga kowane mutum da ya fahimci gaskiya a duk matsayin da ya samu kansa a ciki face ya zama wajibi ya bayyana gaskiyar nan. Domin fadar gaskiyar ba ya kusanto da ajalin mutum, kuma ba ya hana mutum ya samu abin da Allah Ya kaddara masa na abincinsa.”
Game da wannan Hadisi, Al-Imam Muhyiddin Abu Zakariyya Ahmad bin Ibrahim bin Nuhhas Ad-Dimashkiy ad-Dumyatiy, ya fada a cikin littafinsa mai suna: “Tanbihul Gafilina an A’amalil Jahilin wa tahziris-salikina min Af’alil Halikin,” Shafi na 88, inda yake cewa: “A cikin wannan Hadisi akwai kwadaitarwa a kan wajabcin yin gaba-gaba wajen fadar gaskiya da kuma kare ta. Kuma a cikinsa akwai bukatar samun jaruntaka daga bangaren masu da’awa, masu umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna. Ya ci gaba da cewa; “ya zama wajibi mutane su sani, kuma sani na hakika, fadar gaskiya da kare ta ba ya kusanto da ajalin mutum (face lokacin da Allah Ya nufa ya mutu). Kuma fadar gaskiya ba ya hana wa mutum cin abincin da Allah (SWT) Ya kaddara masa samu.” Ya ce, kada mutum ya damu da abin da Shaidan ke jefawa a zuciya na sanya masa rauni da tsoro. Hudubar da Shaican zai rika yi maka yana cewa kada ka fadi gaskiya, kada ka kare ta, idan ka yi haka wane zai kashe ka, ko su wane za su kashe ka, ko wane zai sa a kama ka, ko wane ko su wane za su dake ka, duk wannan shirme ne, domin cutarwa da wani amfani da za su samu kowane mutum an rigaya an kaddara su. Don haka ba abin da zai faru face abin da Allah (SWT) Ya kaddara zai faru ga mutum.”
Hakika Hadisi ingantacce ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafifici daga cikin shahidai shi ne Hamza bin Abdul Mutallib da kuma duk mutumin da ya tashi tsaye ya fuskanci azzalumin shugaba (da kowane irin azzalumi) ya gaya masa gaskiya, ya nuna masa abin da yake yi bai da kyau, sannan bayan fadar gaskiyar aka kashe shi.”
Ya bayin Allah! Wallahi a cikin wannan Hadisi akwai kwadaitarwa a kan yi gaba-gaba da jaruntaka wurin fadar gaskiya da kare ta, koda yin haka zai sa mutum ya rasa rayuwarsa. Irin wannan aiki shi ne aikin da aka kashe Baban Abdurrahman Muhammad Auwal Albani saboda shi. Shi dai tasa ta yi kyau, kuma duniya ta shaida ya cika da kalma mai tsada, kalma mai kyau da duk Musulmi na kwarai yake fatar cikawa da ita. Don haka makasan Albani sai su mutu da bakin ciki, kuma su jira tasu mutuwar domin abu ne da ba makawa sai ya faru, tasu mutuwar insha-Allahu sai ta kasance gara mutuwar kare da jaki a kanta da yardar Allah. Kuma wallahi babu shakka ko kokwanto a kan wannan, sai fa idan sun tuba, Allah Ya shirye su sun bar wannan mummunar hanya na kisan bayin Allah babu gaira babu dalili.
Hazaifatu bin Yaman (RA) yana cewa: “Wani zamani zai zo wa mutuane wanda a cikinsa zai kasance mutane sun fi son rubabbun kayan cikin mushen jaki a kan mutumin da ke yi musu wa’azi yana fada musu gaskiya.”
Ya ku Bayin Allah masu girma! Wallahi, ina yi muku rantsuwa da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Wannan zamani da muke ciki a yau shi ne zamanin da Huzaifah yake maganar zuwansa. Domin a yau, duk wanda ya dauki hanyar jajircewa domin bayyana wa al’umma gaskiya sai ya yi hakuri matuka, domin za a tsangwame shi, mutane za su kyamace shi, za su ki shi, za su ga ya tare musu wasu al’amura, ya hana su holewa, ya hana su yi abin da suka ga da dama, zai kawo musu cikas. Sannan za a jefe shi da kazafi da yi masa karya da kage iri-iri. Za a munana masa zato, za a nufe shi da cutarwa iri-iri, zai yi yawan makiya da masu adawa da shi. Zai yi karancin masoya da abokai. Za a zage shi, za a jefe shi, za a takura masa, zai hadu da matsi iri-iri. Daga nan za a fara tunanin yaya za a yi a rabu da shi, ta yaya za a kauda shi, domin a huta da shi kwata-kwata ko a huta daga da’awarsa – yaya za a yi a raba shi da duniya domin a sarara. Domin ta hanyar hujja da ilimi ya buwaya ya gagara, ya hana su sakat. Ya hana su motsi, ya zamar musu karfen kafa, yana bayyana wa jama’a sharrinsu. Daga karshe sai a daure shi, kamar yadda ya faru da Baban Abdurrahman a can baya. Sannan sai maganar a kashe shi, kamar yadda aka yi masa. Fa inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Allah Ya jikanka, Ya gafarta maka Ya haskaka kabarinka, Ya kunyata tare da tozarta magabtanka, ya shahidi Baban AbdurRahman.
Wata rana Ka’abul Akhbar ya ce da Abu Muslim Al-Khawlaniy (a lokacin da Abu Muslim ya tashi tsaye wurin fada wa al’umma gaskiya). “Ya Abu Muslim mene ne matsayinka a cikin mutanenka? Yaya suka dauke ka? Sai Abu Muslim ya ce; “Ba komai tsakanina da su sai alheri; sai Ka’abul Akhbar ya ce “amma a cikin Attaura ba haka muka samu ba, mun samu ne cewa duk mutumin da ke tsage gaskiya komai dacinta zai sha wahala, zai hadu da tsangwama iri-iri, mutane za su ki shi. Sai Abu Muslim ya ce: “Lallai abin da Attaura ta bayyana shi ne gaskiya, Abu Muslim kuwa shi ne bai fadi gaskiya ba.”
Ya ku bayin Allah! Imam Muslim ya fitar da Hadisi a cikin sahihisa, cewa Annabi (SAW) ya ce: “Musuluncin nan ya faro ne kamar bako, kuma da sannu nan gaba zai sake komawa bako kamar yadda ya faro. Madalla da baki, itaciyar Aljanna (tuba) za ta kasance ga baki. Sai sahabbai suka tambayi Manzon Allah, su wane ne baki ya Manzon Allah? Sai ya ce: “Mutanen kirki ne salihai a cikin tsakiyar mutanen banza masu yawa. Wadannan mutanen kirkin zai kasance masu adawa da su sun fi masu son su yawa.”
Imam Sufyan As-Sauriy (RH) ya ce: “Idan ka ga malami mai yawan masoya, mai yawan abokai, to ka tabbata ya kauce hanya kuma ba ilimi yake yadawa ba. Sai aka tambayi Sufyan As-Sauriy ta yaya haka zai kasance? Sai ya ce: “in dai har Malami zai fadi gaskiya, to, mutane za su ki shi, za su yi adawa da shi!”
Ya ku bayin Allah! Wallahi da zan yi ta kawo misalan ire-iren wadannan abin zai tsawaita. A  karshe abin da zan ce shi ne: “kowane malami ya ji tsoron Allah ya fadi gaskiyar da ya sani kuma ko a kan wane ne ko su wane ne. Domin ko ya tsaya a kan gaskiya ko bai tsaya ba, zai mutu, kuma ba wanda zai mutu sai kwanansa ya kare.
Ina kira ga iyalai da daliban Malam da dukkan al’ummar Musulmin Najeriya mu yi hakuri mu dauki dangana. Da ma Allah (SWT) Ya yi alkawarin sai Ya jarraba imaninmu: “Ashe, mutane suna zaton a bar su a kyale su, kawai don sun ce “mun yi imani,” alhali kuwa ba za a jarrabe su ba?  Kuma wallahi hakika mun jarrabi wadanda ke gabaninsu domin Allah Ya san wadanda suka yi gaskiya kuma Ya san su wane ne makaryata.” (Ankabut: 2-3). Allah Ya sake cewa: “Kuma lallai ne wallahi Muna jarraba ku da wani abu daga tsoro (rashin zaman lafiya) da yunwa da nakasar dukiya da ta ’ya’yan itace. Kuma ka yi bushara ga masu hakuri. Wadanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce: “Lallai mu daga Allah muke, kuma lallai zuwa gare Shi mu masu komawa ne.” Wadannan akwai albarka da addu’a a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma wadannan su ne shiryayyu.”  (Bakara: 155-157).
Kuma wallahi, ba za a taba gushewa ba a cikin al’umma ana samun wadanda za su jajirce, su ci gaba da taimakon gaskiya da masu gaskiya har karshen duniya. Wannan alkawari ne na Allah (SWT). Saboda haka ya ku bayin Allah! Ku kwantar da hankalinku, kuma ku sani, masu yin wadannan kashe-kashen a cikin al’umma, suna bata lokacinsu ne kawai. Manzon Allah (SAW) ya fada a Hadisin da Buhari da Muslim suka ruwaito cewa; “wata jama’a ba za ta taba gushewa daga cikin al’ummata ba, tana taimakon gaskiya da kare ta. Mai adawa da su da wanda ke sabani da su, ba zai taba cutar da su ba. Suna kan haka ba gudu ba ja da baya har hukuncin Allah ya kasance.”
Imam Murtada Muhammad Gusau
08038289761