✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe malamai ba zai hana addini ci gaba ba (1)

Masallacin Juma’a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi Huduba ta FarkoGodiya ta tabbata ga Allah wanda ya fada a cikin littafinsa mai girma: “Kada ka yi…

Masallacin Juma’a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi

Huduba ta Farko
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya fada a cikin littafinsa mai girma: “Kada ka yi tsammanin wadanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne su, a wurin Ubangijinsu. Ana ciyar da su.” (Al-Imran:169).
Ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Kuma Ya fada a wani wurin cewa: “Kada ku ce ga wadanda ake kashewa a kan tafarkin Allah: “Matattu ne.” A’a, rayayyu ne, sai dai ku ba ku sani ba.” (Bakara:154). Kuma ya sake cewa: “…Kuma wadanda aka kashe a kan tafarkin Allah, to, ba zai tozartar da ayyukansu ba.  Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata halayensu. Kuma Ya shigar da su Aljannah (wadda) Ya siffanta ta a gare su.” (Muhammad: 4-6).
Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad (SAW) bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda ya fada a Hadisin Sahlu da ke cikin Sahihu Muslim, cewa;
“Duk wanda ya roki Allah (SWT) shahada da gaskiya, to Allah zai kai shi matsayin shahidai koda kuwa a kan shimfidarsa ya mutu.” Allah Ya yi dadin tsira da aminci a gare shi da iyalin gidansa da sahabban sa da duk wanda ya bi tafarkinsu da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah masu girma! Da farko ina bude hudubar wannan rana da fadar “Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’un!” Kamar yadda muka sani, ranar Asabar da ta gabata, 1 ga Rabi’us Sani, shekara ta 1435 Bayan Hijirah, wadda ta yi daidai da 1 ga Fabrairun 2014, wani mummunan labari mai cike da tashin hankali da firgici ya same mu da misalin karfe 10:00 na dare, cewa wasu ’yan bindiga, ’yan ta’adda, matsorata,wawaye, marasa imani da tausayi da tsoron Allah, sun harbi Baban Abdurrahman, Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya, shi da matarsa da wasu daga cikin ’ya’yansa. Bayan da ya gama darasin Sahihul Bukhari, a kan hanyarsa ta komawa gida. A nan take Allah Ya karvi ran matarsa da dansa Abdullahi. Shi kuma Malam aka garzaya da shi zuwa asibiti, bayan minti biyar kuma muka sake samun labari cewa shi ma Malam Allah Ya karvi ransa a kan hanyarsu ta zuwa asibiti saboda haka sai aka juya da gawarsa zuwa gida.
Sheikh Albani ya rasu yana da shekara 54, kuma ya bar mata uku da ’ya’ya sama da 20. Kuma ya bar dubban dalibai a baya, ciki da wajen kasar nan. Allah Ya gafarta masa, amin.
Ya ku Musulmi! Lallai wannan kisan gilla da aka yi wa Sheikh Auwal Albani al’amari ne da duk wani mutum mai tsoron Allah dole ya girgiza shi. Amma babu abin da za mu ce illa, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
Malam taka ta yi kyau, kuma lallai burinka ya cika. Saura da me? Sai mu ce don Allah wadanda suka aikata wannan aika-aika Ga malam, wadanda suka aikata wannan danyen aiki, su dawwama a duniya kada su mutu. Su hana mutuwa daukar rayukansu idan ta zo musu. Wadanda suka aikata wannan aiki da duk wani mai hannu a ciki da duk wadanda suka yi murna da farin ciki, suka ji dadin abin da aka aikata ga Malam, don Allah muna rokonsu, su dawwama a duniya har abada kada su mutu idan har zai yiwu. Idan ba hauka ba da wawanci da jahilci ba, mutuwar da kowa dole sai ya dandane ta, mene ne na gaggawar kashe wani?
Bawan Allahn nan tunda ya taso yana saurayi matashi yake hidimar addini na karatu da karantarwa. Bai yi wa kowa laifi ba, bai cuci kowa ba, bai ci kayan kowa ba, bai zalunci kowa ba, amma don zalunci kawai an kashe shi. Kuma ba don komai ba wallahi illa kawai don gaskiyar da yake isarwa zuwa ga al’umma da ta shafi addininsu da kuma rayuwarsu. To, ba komai shi Malam gaba ta kai shi. Addu’ar da ya dade yana yi ta Allah Ya azurta shi da shahada, ita ce Allah Ya amsa. Kuma muna da yakinin cewa Malam dan Aljannah ne, ba don komai ba sai don fadar Annabi (SAW) cewa: “Duk wanda ya kasance maganarsa ta karshe ta zama la’ilaha illallah, to ya ma shiga Aljannah.” Malam kuwa har Allah Ya karvi ransa yana Kalmar Shahada. Ka ga a nan suna ganin sun yi sharri amma a hakikanin gaskiya shi alheri ne a gare shi.
Ya ku bayin Allah! Lallai ya kamata mu sani wallahi duk wani mai tunanin cewa zai hana yaduwar gaskiya ta hanyar kashe masu fadarta, to, lallai wannan mutum ya makara! Domin idan haka ne da tun lokacin Annabawa da Manzannin Allah gaskiya ta kare, saboda kisan gilla domin yada addini ya faro ne tun lokacinsu.
Idan za mu iya tunawa ’yan uwana masu girma! An yi yunkurin kashe Annabi Ibrahim (AS) saboda gaskiya.  An yi yunkuri ba iyaka don a kashe Annabinmu Annabi Muhammad (SAW). Annabin Allah Musa (AS) an yi taron tattauna yadda za a kashe shi, amma Allah Ya kubutar da shi. Ina As’habul Kahfi (Ma’abuta Kogo) da suka yi imani da sakon da Manzanin Allah suka zo da shi? An biyo su za a kashe suka gudu da imaninsu suka shiga kogo. Kai wasu Annabawan Allah ma umurtarsu aka yi su kwashe mutanen da suka yi imani da su su bar gari su koma wani garin don tsira da rayukansu da addininsu. Kamar Annabi Musa da Annabi Lut (AS) da sauransu. Annabi Ibrahim (AS) wuta aka hura za a kone shi da ransa ba don komai ba, sai saboda gaskiya. Kuma a cikin wadanda za su yi masa wannan ta’addanci har da mahaifinsa fa?
Ya ku Bayin Allah! Ina yi muku rantsuwa da Allah Wanda raina yake hannunSa, a rana daya Banu Isra’ila sun yanka Annabawa sama da arba’in. Sannan yaya labarin Annabi Zakariyya da Annabi Yahaya (AS)? Shin ba azzalumai suka yanka su ba saboda kiransu zuwa ga hanyar Allah tare da kiransu su bar varna ba?
Ya ku Musulmi! Shin za mu iya tunawa da wahalar da Annabi Yusuf (AS) ya sha (zaman fursuna) a hannun azzalumai ba don komai ba sai don gaskiya? Za mu iya tuna irin kisan gillar da Fir’auna ya sa aka yi wa masu sihirinsa saboda sun gane gaskiyar da Annabi Musa ya zo da ita?
Ya ku bayin Allah! Ina labarin Musaikah da Umaimah, bayin shugaban munafukai Abdullahi bin Ubay bin Salul? Wadanda yake tilastawa su yi karuwanci su kawo masa kudi, amma da sakon musulunci ya shige su, suka ce masa su ba za su sake yin karuwanci ba, ya sa aka kashe su? Ina As’habul Ukhdud (Mutanen Ramin Wuta) da azzalumin shugaba ya sa aka hura wuta aka rika jefa mutane ciki ana kone su da ransu saboda gaskiya? Yaya maganar yaro da sarki da boka? Yaron da ya sadaukar da kansa domin al’umma ta fahimci gaskiya? Kamar yadda Albani ya sadaukar da rayuwarsa domin al’ummarsa ta fahimci addininta da rayuwarta? Karanta Suratul Buruj, sannan karanta kissar tana cikin Sahih Muslim.
Ya ku bayin Allah! Shin don Allah wace irin wahalarwa ce sahabban Annabi (SAW) ba su gani ba saboda fadar gaskiya da jajircewarsu a kan dora al’ummarsu a kan daidai?
Za mu iya tuna mutane irinsu Khabbab bin Al-Arsi (RA)?  Da Bilal bin Rabah (RA)? Da irin wahalar da su da makiya gaskiya suka yi kuwa? Yaya iyalin Yasir wato Sumayyah, wadda ta fara shahada a tarihin Musulunci da danta Ammar? Shin ina su Malama Zin-Nirah da sauransu? Macen da aka tsiyayar da idanuwanta da ranta, saboda kawai imaninta da Allah?
Shin ko ’yan uwana masu girma za su iya tuna bawan Allah Habib bin Zaid Al-Ansari (R.)? Mutumin da Musailamah makaryaci ya tambaye shi, shin ka yi imani cewa Annabi Muhammadu (SAW) Manzon Allah ne? Ya ce eh! Sannan ya sake tambayarsa, ka yi imani ni Musailamah Manzon Allah ne? Sai Habib ya ce ban ji ka ba. Da jin haka sai Musailamah ya sa aka rika yankan naman jikinsa guntu-guntu har sai da ya mutu.
Yaya labarin Abdullah bin Huzaifah (RA) da irin kisan gillar da Sarkin Rum ya yi masa? Yaya karon-battar Bawan Allah Abu Muslim Al-Khawlani da makaryaci Al-Aswad bin kays wanda ya yi da’awar Annabta ta kasance?
Ya ku Bayin Allah! Shin mun manta da irin yadda wawa, azzalumi, Bayahude, kuma Bamajuse dan kasar Yaman mai suna Abu Lu’a-Lu’ata Almajusi ya kashe Halifan Manzon Allah na biyu wato Umar (RA) a masallaci ana Sallar Asuba? Ko mun manta da yadda wawaye suka yi wa Usman (RA) kisan gilla a gidansa da azumi a bakinsa yana karatun Alkur’ani? Ko mun manta yadda wani wawan mai suna Abdurrahman bin Muljam ya kashe Halifan Manzon Allah na hudu wato Ali (RA)?
Ya ku bayin Allah! Yaya labarin kisan gillar da aka yi wa wasu daga cikin iyalin Gidan Manzon Allah? Yaya kisan gillar da Hajjaj bin Yusuf As-Sakafi ya yi wa Sa’id bin Jubair (RH)? Ya Allah muna rokonKa don tsarkin sunayenKa Ka tona asirin wadanda ke yi wa al’umma wannan ta’addanci, amin.
Imam Murtada Muhammad Gusau
08038289761