Babban Masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
An karbo Hadisi daga Mu’azu bin Jabal (R.A) ya ce: “Wata rana Annabi (SAW) ya yi wata Sallah mai tsawo (ya tsawaita ta), bayan ya kare, sai muka ce: “Ya Manzon Allah, yau ka tsawaita sallah. Sai ya amsa cewa: “Na yi Sallah ce da ke cike da kwadaitarwa da firgitarwa. Na roki Allah Ya yi min abubuwa uku game da al’ummata, sai Ya amince mani da guda biyu, Ya ki yarda da daya. Na roki Allah kada Ya dora makiyi a kan al’ummata daga waje, Ya yarda mani wannan. Na roki Allah kada Ya sa al’ummata su rika yakar junansu (suna kisan juna), amma Allah bai karbi wannan ba.”
Kuma Muslim ya fitar da shi, daga Sa’ad bin Abu Wakkas (R.A): “Lallai Manzon Allah (SAW) ya fuskanci jama’arsa wata rana: A wata ruwaya: “Wata rana Annabi (SAW) na cikin wasu jama’a daga sahabbansa da ya kawo daidai masallacin Banu Mu’awiya, sai ya shiga ciki ya yi Sallah raka’a biyu. Sai muka bi shi muka yi sallar tare a bayansa. Da ya gama sai ya yi wata irin doguwar addu’a sannan ya zo wurinmu ya ce: “Na roki Allah abubuwa uku, ya karbi biyu, bai karbi daya ba…” har zuwa karshen Hadisin. Muslim da Ibnu Abu Shaibah da Ahmad ne suka ruwaito.
Ya ku Bayin Allah! Duk wadannan Hadisai suna karantar da mu tare da nuna mana cewa, na daga alamun kusantowar Alkiyama, irin yadda al’umma za ta rika kisan juna tana zubar da jinin juna, kamar yadda ke faruwa a cikin kasashen Musulmi a yau, ciki har da wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Mu dubi abin da ke faruwa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa. Koda a ce misali, akwai makiya wannan al’umma da ke bayar da taimako ta karkashin kasa da gudunmawa domin rusa ta, to lallai za ka ga cewa, masu zartarwa tare da aiwatar da wannan aika-aika, Musulmi ne. Domin ba yadda za a yi galaba a kanmu sai an hada da namu. An wayigari a yau, sun addabi ’yan uwansu, suna bi kauye-kauye suna kisan bayin Allah tare da kone kauyen gaba daya. An wayigari makiya wannan al’umma suna daukar nauyinsu, suna ba su kudade da makamai don su yaki jama’arsu, saboda sun kasance mutane ne ba masu kishin al’ummarsu ba.
Ya ku bayin Allah! Abin da zai kara fito mana da abin fili shi ne, yanzu a misali, in dai har abin da jami’an tsaro na farin kaya (SSS) suka yi, ranar Litinin da ta gabata, 3 ga Maris, na gabatar da wasu mutum bakwai da ake zargi da kisan Sheikh Albani Zariya, ya zama gaskiya, to wannan zai kara maka imani da yakini da kauna tare da gaskata Manzon Tsira dan Abdullahi (SAW), duk da cewa mun yi imani, imanin da babu shakka ko kokwanto a cikinsa cewa, shi mai gaskiya ne kuma abin gaskatawa.
A yau an wayigari, a duk lokacin da ka karanta, ko ka saurara ko ka leka, ko ka kalli abin da ke faruwa na tashin hankali da zubar da jinin bayin Allah da kone musu gidaje a kafafen watsa labarai irin su rediyo da jaridu da mujallu da yanar gizo da akwatin talabijin, ina rantsuwa da Allah Wanda ba abin bautawa da gaskiya sai Shi, sonka da Manzon Allah (SAW) zai karu. Imaninka da yakininka a kan cewa lallai babu wani abu da ya faru ko zai faru nan gaba a duniya gabanin tashin Alkiyama, face ya ba da labarinsa. Kuma abin ya faru kamar yadda ya ba da labari (SAW), mai gaskiya abin gaskatawa, wanda ba ya magana da son zuciya. Hakika duk wannan zubar da jini da yake-yake, Manzon Allah (SAW) ya ba da labarin aukuwarsu.
Ya ku bayin Allah! Shin kuna zaton duk wadannan mutane bakwai da jami’an tsaro suka gabatar game da zargin kisan Albani ba Musulmi ba ne? Shin kuna zaton wadanda ke kai hare-hare a kauyukan Borno da Yobe da Adamawa ba Musulmi ba ne? Wallahi dukansu Musulmi ne, da makiya wannan al’umma ke amfani da su domin rusa ta. Kuma abin da muke cewa shi ne, su sani za mu ci gaba da addu’o’i da alkunuti a masallatanmu da gidajenmu insha-Allahu, har Allah Ya yaye mana wannan musiba.
Sannan ya ku al’umma! Ku sani, Allah ba zai karbi addu’o’inmu da kunutinmu ba har sai mun tuba, mun nemi gafarar Allah daga zunubanmu, mun gyara halayenmu, mun bar miyagun dabi’u da munanan ayyuka. Sai mun kaskantar da kawunanmu zuwa ga Allah, mun nuna mu ba kowa b ane a gaban Allah, sai Allah Ya tausaya mAna. Sai mun daina zalunci da cutar mutane, sai Allah Ya kawo mana dauki. Mu ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Mu nemi kusancin Mahaliccinmu, mu rungumi shiriyarSa, mu tabbatu a kan gaskiya, mu koma zuwa ga Allah baki daya, ya ku muminai! Ko ma samu rabauta.
Ya Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka daukaka Najeriya da ’yan Najeriya, Ka halakar da makiyanKa, makiya addininKa, Ka taimaki bayinKa salihai a duk inda suke.
Ya Allah Ka ruguza taron munafunci da munafukai, Ka kunyata kuma Ka tozarta kuma Ka wulakanta azzalumai a duk inda suke. Ya Allah! Duk wanda yake da hannu a kisan ’yan uwanmu da ke Borno da Yobe da Adamawa da sauran wurare, ka sanya firgita da razana da tsoro da dimuwa da tabin hankali da rudewa a rayuwarsa, kamar yadda firgici da tashin hankali ke kama marar imani idan ya zo mutuwa.
Ya Allah! Duk wanda ke da hannu wurin cutar da bayinKa, Ka hana shi barci, Ka hana shi kwanciyar hankali, Ka jarrabe shi da ciwon mantuwa, Ka kara tona masa asiri duniya da Lahira.
Ya Allah! Kai Ka ce mu roke Ka za Ka amsa mana, Ya Allah! Kana fushi da masu girman kai daga rokonKa, kuma Ka tabbatar lallai za su shiga Jahannama suna kaskantattu. Ya Allah! Ka saukar da zaman lafiya a kasashen Musulmi da jihohinsu da gidajensu da kasarmu Najeriya baki daya.
Ya Allah! Ka tausaya mana, don albarkar sunayenKa tsarkaka da siffofinKa madaukaka, wadanda muka sani da wadanda ba mu sani ba. Ya Allah! Mun tuba, mun tuba, mun tuba, mun bi Ka, muna neman afuwarKa, Ka tausaya mana, don rahamarKa da jinkanKa da tausayinKa, ya mafi tausayin masu tausayi ya Ubangijin halittu!
Ina fadar wannan magana tawa, ina mai neman gafarar Allah ga kaina da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Imam Murtada Muhammad Gusau
Babban Masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
08038289761